Nollywood: Hukumar Fina Finai ta Dauki Mataki da Musulmai Suka Soki Bata Sunan Hijabi a Fim
- Hukumar tace fina-finai ta kasa (NFVCB) ta waiwayi koken wasu musulman kasar nan a kan sabon fim din Nollywood, indata ce ta dauki mataki
- Kungiyar kare hakkin musulmi ta kasa (MURIC) ce ta fara bayyana damuwa a kan yadda aka nuna mata da shigar Islama su na fashi
- Hukumar NFVCB ta cikin sanarwar da ta fitar ta ce tuni ta tuntubi wadanda suka shirya fim din, kuma za a gyara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Bayan kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bayyana rashin dacewar sabon fim din Nollywood, hukumar tace fina-finai (NFVCB) ta dauki mataki.
A ranar Alhamis ne kungiyar MURIC ta bayyana cewa fim din zai kara jefa kyamar mata musulmi a zukatan al'ummar kasar nan, saboda haka a gaggauta dakatar da fitar da shi.
A sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa ta ji kiraye-kirayen musulmin kasar nan kuma tuni ta tuntubi wadanda su ka shirya shirya fim din domin daukar matakin gyara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba a saki fim din ba," NFVCB
Hukumar ta ce fina-finai ta NFVCB ta bayyana cewa ta gana da wadanda su ka shirya sabon fim din Nollywood da ya jawo damuwa ga wasu musulmin kasar nan saboda yadda aka nuna shigar mata musulmi ta mummunar fuska.
NFCVB ta ce bincikenta ya tabbatar da cewa har yanzu ba a kai ga sakin fim din ba, saboda haka za a dauki matakin gyara kura-kuran da aka gano a cikin fim din.
Tuni wasu musulmin kasar nan su ka yi maraba da matakin da NFCVB ta dauka, ciki har da tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ta shafinsa na X.
MURIC ta soki sabon fim din Nollywood
A baya mun ruwaito yadda wata kungiyar kare hakkin musulmin Najeriya (MURIC) ta bayyana takaici a kan sabon fim din Nollywood da ake shirin saki, wanda ke nuna mata rike da mugayen makama su na fashi.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya ce nuna mata cikin cikakkiyar shigar musulunci dauke da mugayen makamai zai kara jefa tsangwamar musulmin masu sanya suturar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng