"Mijina Ya Daina Biya Mun Buƙata, Yana Zargi Na da Zina" Matar Aure Ta Nemi Saki a Kotu

"Mijina Ya Daina Biya Mun Buƙata, Yana Zargi Na da Zina" Matar Aure Ta Nemi Saki a Kotu

  • Wata matar aure ta shaida wa Kotu a Ilorin, babban birnin jihar Kwara cewa ta gaji da zama da mijinta saboda yana zarginta da zina
  • Matar mai suna Rashidat Bashir ta ce wanda taƙe kara ya daina ɗaukar nauyin iyalansa a matsayinsa na mahaifin ƴaƴa uku da ta haifa
  • Sai dai mijin ya roƙi Kotun kada ta raba su saboda har yanzun yana ƙaunar matarsa kuma bai shirya rabuwa da ita ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kwara - Wata matar aure uwar ‘ya’ya uku, Misis Rashidat Bashir, a ranar Talata, ta bukaci wata kotun yankin a Ilorin ta raba aurenta da mijinta, Ashomu Bashir.

Rikicin ma'aurata a Kotu.
"Mijina Baya Biya Mun Buƙatu, yana zargi na da neman maza" Mata ta nemi saki a Kotu Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

A rahoton da jaridar Daily Trust ta tattaro, matar ta nemi Kotu ta datse igiyoyin aurenta da Bashir ne saboda yana zarginta da cin amana da neman maza da lalata.

Kara karanta wannan

Amarya ta cinnawa gidan mijinta wuta kan abu 1 a Adamawa

Meyasa take neman rabuwa da mijinta?

Matar ta kuma shaida wa Kotun cewa ta gaji da zaman auren, inda ta bayyana cewa tuntuni wanda take ƙara ya daina sauke haƙƙinsa a matsayin uban ƴaƴanta da kuma miji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin da ta yi wa Kotun, Rashidat ta ce:

"Ina son ya sake ni saboda na gaji da wahala da kuma damuwa da yawan tunani. Ni kaɗai ke ɗaukar nauyin ciyar da gidan da kulawa har da biyan kuɗin makarantar 'ya'yanmu uku."
"Saboda miji na ba ruwansa da kula da yaran kamar yadda ya rataya a kansa. Ina kasuwancin siyar da magunguna daga nan zuwa can na yi amfani kuɗin wajen siyo abinci da sauran buƙatun gida."
"Amma duk da haka mijina ba shi da aiki sai ya riƙa jifa na da zargin cin amana, yana zargi na da aikata zina da wasu mazan."

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana tarin gwaramar da shugabannin da suka gabacesa suka bar wa gwamnatinsa

Ina kaunar matata har yanzu

A nasa ɓangaren, wanda ake ƙara watau mijin matar, Ashomu Bashir, ya roƙi Kotu kada ta aminta da bukatar mai ɗakinsa ta raba auren.

Ya kuma shaida wa alkalin cewa har yanzun yana ƙaunar matarsa kuma bai shirya rabuwa da ita ba, kamar yadda jaridar The Angle ta ruwaito.

Yajin Aikin NLC Ya Kawo Cikas a Kotun Abuja

A wani rahoton na daban An samu tsaiko a shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a babbar Kotun Abuja.

Hakan ya faru ne sakamakon yajin aikin da ƙungiyar ma'aikatan shari'a (JUSUN) ta shiga a reshenta na babbar Kotun Abuja bisa umarnin ƙungiyar kwadago NLC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel