Magidanci Dan Najeriya Ya Kadu Bayan Matarsa Ta Tafi Da 'Ya'Yansa Ba Tare Da Saninsa Ba

Magidanci Dan Najeriya Ya Kadu Bayan Matarsa Ta Tafi Da 'Ya'Yansa Ba Tare Da Saninsa Ba

  • Wani magidanci ɗan Najeriya ya bayyana cewa watarana ya dawo gida kawai ya tarar matarsa da ƴaƴansa ba su a gida
  • Daga nan ne ya fahimci cewa matarsa da suka yi shekara takwas tare, ta kwashe yaran ta tafi da su
  • Ya bayyana cewa har yanzu a shirye yake su sasanta sannan ya yi fatan cewa bai makara ba wajen ganin sun sasanta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani magidanci ɗan Najeriya, Wale Adebayo, ya bayyana yadda matarsa ta kwashe ƴaƴansa ta bar masa gida tare da su.

Wale ya bayyana labarinsa ne a Twitter lokacin da yake ta'aziyya ga @Temmy_omoileri wacce ta rasa mijinta.

Magidanci ya koka bayan matarsa ta tafi da yayansu
Hotunan an yi amfani da su ne kawai domin misali amma ba su da alaka da abin da yake a cikin labarin. Hoto: @RealAdebayo
Asali: Getty Images

Wale ya bayyana cewa shekara biyu kenan tun faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa sun kwashe shekara takwas suna rayuwar aure da matar ta sa.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Boye Lamba Ya Yi Wa Budurwarsa Magana, Ta Fada Masa Cewar Bata Da Saurayi

A cewarsa, a auren na su sun riƙa samun saɓani amma suna sasantawa daga baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wale ya ƙara da cewa har yanzu ƙofa a buɗe take ya sasanta da matarsa sannan yana yi mata addu'a tare da ƴaƴansa.

A kalamansa:

"Shekarunmu takwas muna zaman aure, mun samu ƙalubale. Wata rana kawai na dawo gida sai na ga ta kwashe kaya ta tafi tare da yaran. Shekara biyu kenan yanzu, zuciya ta a shirye take mu sasanta. Ina yi mata addu'a da iyalanmu. Na yi kewar iyalaina. Ina fatan ban makara ba."
"Ina yi miki ta'aziyya Temmy"

Ƴan soshiyal midiya sun tausayawa Wale Adebayo

@queensomto ta rubuta:

"Idan ba ta dawo gare ka ba, kaje neman iyalanka."

@UcheKlasique ya rubuta:

"Ka daure ka nemo ta ku sasanta. Abin da na karanta yanzu ya sanya ni zubar da hawaye. A ƙarshe dai su kaɗai gare ka su ma kai kaɗai garesu."

Kara karanta wannan

Matan zamani: Miji ya sha bulala saboda yiwa matarsa wani babban laifi, jama'a sun girgiza

@Yurmyth ya rubuta:

"Ka daure ka nemo ta ku sasanta idan har tana nan."

@odun102 ya rubuta:

"Allah ya sanya ku sasanta kan ku. Ka cigaba da nemanta domin ku shirya idan ba wani ta namijin ta bi ba. Wasu lokutan kalmar 'yi haƙuri' na magance matsaloli masu yawa."

Babbar Kawa Ta Yi Cin Amana

A wani labarin kuma wata matar aure ta koka kan irin cin amanar da babbar ƙawarta wacce ta aminta da ita, ta yi mata.

Matar auren dai ta je wurin bikin mijinta lokacin da zai ƙara aure, kawai sai ta tarae babbar ƙawarta ce amaryar da zai aura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel