"Ina Cikin Damuwa" Gwamnan PDP Ya Faɗi Halin da Yake Ciki Saboda Rikicin Siyasar Jiharsa

"Ina Cikin Damuwa" Gwamnan PDP Ya Faɗi Halin da Yake Ciki Saboda Rikicin Siyasar Jiharsa

  • Gwamna Fubara na jihar Ribas ya koka kan rikicin siyasar jihar wanda a cewarsa yana taɓa rayuwarsa da ta iyalansa
  • Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike, sun samu saɓani kan yanayin jagoranci da jan akalar siyasar jihar mai arzikin man fetur
  • Ya ce duk da jama'a na cikin farin ciki amma shi yana yaƙe ne kawai amma abun yana damunsa sosai a cikin rai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya bayyana yadda rikicin siyasar jihar ke yi masa lahani a rayuwarsa ta yau da kullum.

Gwamna Fubara da tsohon gwamnan da ya gabata, Nyesom Wike, suna takun saƙa da juna kan tafiyar da harkokin mulki da jan ragamar siyasar jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka shugabannin matasa 2 a jihar PDP

Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamna Fubara: Rikicin Siyasar Jihar Ribas Yana Taba Ni da Iyalaina Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

A rahoton The Nation, yayin da yake jawabi a cocin St Paul’s Anglican da ke garin Opobo, ƙaramar hukumar Opobo Nkoro ta jihar, Fubara ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina jin nauyi a raina, ba abu ne mai sauƙi ba sabida na rasa kalmar da zan muku bayanin yadda nake ji a raina."

Fubara ya yi wannan furucin ne a wurin taron addu'o'i na musamman da aka shirya a cocin domin murnar nasarar da ya samu a Kotun Ƙolin Najeriya.

Taron ya zo rana ɗaya da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Gwamna Fubara, wanda ya cika shekaru 49 cif-cif a duniya.

Yadda rikicin Ribas ya taɓa iyalan Fubara

A jawabinsa a wurin taron. Gwamna Fubara ya ce iyalinsa na shan wahala matuƙa saboda rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.

Ya shaida wa mahalarta wurin cewa akwai waɗanda ya kamata su halarci taron amma ba su halarta ba, da alama yana nufin Mista Wike, wanda yanzu shi ne ministan Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kisan da aka yi wa sarakunan gargajiya, ya bayar da sabon umarni

A rahoton Premium Times, gwamnan ya ce:

"Bari na tambayeku, idan na kalli fuskokin ku ina ganin kuna cikin murna da farin ciki, amma tambayar da zan muku ita ce, shin ni ina farin ciki? Shin Allah zai baka kyauta da ni'ima kuma ya haɗa da ƙunci?"

Nan take waɗanɗa suka halarci taron suka haɗa baki suka amsa da cewa. "A'a"

Fubara ya ci gaɓa da cewa, "sabida haka idan na kalli farin cikin da kuke yi duk da nauyin da nake ji a rainna, sai na samu karfin guiwar yin farin ciki, halin da nake ciki kenan, ba abu ne mai sauki ba."

Majalisar Edo ta dakatar da mutum 1

A wani rahoton kuma Kakakin majalisar dokokin jihar Edo ya dakatar da ɗan majalisa ɗaya na tsawon wata uku bisa laifin yunkurin raba kan ƴan majalisa.

Haka nan kuma majalisar ta amince da buƙatar Gwamna Obaseki na PDP na ciyo bashi domin gudanar da wasu ayyuka a jihar Edo da Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel