Budurwa Za Ta Yi Wuff da Abokin Saurayinta, Ta Saki Zafafan Hotunan Kafin Aure

Budurwa Za Ta Yi Wuff da Abokin Saurayinta, Ta Saki Zafafan Hotunan Kafin Aure

  • Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da ta sanar da jama'a game da bikinta mai zuwa
  • Da take yada hotunan kafin aurensu, mai shirin zama amaryar ta bayyana cewa angonta ya nemi aurenta ne yayin da take soyayya da abokinsa
  • Kalaman nata ya janyo cece-kuce daban-daban, inda wasu suka caccaketa kan cin amana, wasu kuma sun taya ta murna

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Favour Okenwa, wata matashiya yar Najeriya, ta sanar da labarin aurenta mai zuwa kuma lamanta sun haddasa cece-kuce tsakanin mutane.

A wata wallafa da ta yi a dandalin Facebook a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, matashiyar ta mato kan angon nata sannan ta saki katin gayyata zuwa waje daurin auren nasu dauke da hotunan kafin aurensu guda biyu.

Kara karanta wannan

"Ban iya bacci ba": Budurwa ta fashe da kuka bayan ta gano saurayinta na shekaru 3 ya yi aure

Masu shirin zama mata da miji
Budurwa Za Ta Yi Wuff da Abokin Tsohon Saurayinta, Ta Saki Zafafan Hotunan Kafin Aure Hoto: Favour Okenwa
Asali: Facebook

Ta shiga soyayya da wani alhalin tana tare da wani

A cewar Favour, soyayyarsu ta fara da rashin tabbass, amma sai ga shi zai kare a aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take bayyana angon nata a matsayin 'mai taurin kai', Favour ta tuna yadda ya nemi soyayyarta yayin da take soyayya da abokinsa.

Amaryar ta nuna soyayyar da take yi wa sahibin nata, tana mai cewa ta fi kowa farin ciki kuma tana gode masa da ya zabe ta.

Ta bayyana cewa an tsara auren a ranar 4 ga watan Janairun 2024.

Jama'a sun yi martani

Hilz Beatz ta ce:

"Ke da bakinki kika fadi abubuwan da ba a tambaye ki ba...wanne ne....ya nemi aurenki alhalin ya sani karara cewa kina soyayya da abokinsa. Wani irin aboki ne wannan?
"Kuma kina tunanin soyayya da abokai biyu yana...kada na yi magana dai....don Allah ba za mu zo ba."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

Blessing Cyril ta ce:

"Baaaba kada ka yarda da kowa faaa.
"Idan masoyinka na soyayyar da wani, ka tarwatsa shi.
"Menene wannan.
"Na taya ku murna."

Kelechi Okwor ya ce:

"Kina da karfin hali fa....kenan kin rabu da abokinsa sannan kika bi shi saboda yana da taurin kai."

Michael Sunday Jude ya ce:

"Baaaba wannan gayen bai da lafiya.
"Ya caki abokinsa sannan ya karbe ki daga hannunsa.
"Abun akwai ciwo, na tuna lokacin da mutumina ya yi mun irin wannan a 2010.
"Na yi kuka, na koka, na ciza hakora sannan na fara daga farko, kuma kun san ne, yanzu ina da masoyiyar da tafi kowacce."

Saurayi ya ci amanar budurwarsa

A wani labarin, mun ji cewa wata budurwa yar Najeriya ta koka yayin da ta sanar da cewar saurayinta na shekaru uku ya auri wata daban a kwanan nan.

Matashiyar, @sexysica_, ta magantu kan soyayyarsu a TikTok yayin da ta dungi zubar da hawaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel