“Na Kama Yayata Tana Cin Amanar Mijinta”: Budurwa Ta Shiga Rudu Bayan Ta Karbi N5m ‘Toshiyar Baki’

“Na Kama Yayata Tana Cin Amanar Mijinta”: Budurwa Ta Shiga Rudu Bayan Ta Karbi N5m ‘Toshiyar Baki’

  • Wata ‘yar Najeriya ta shiga cikin rudani bayan da ta kama wasu ma’aurata suna cin amanar junansu a lokuta daban-daban
  • Ta sake shiga rudu ne yayin da matar, wacce 'yar'uwarta ce, ta bata naira miliyan 5 toshiyar baki don kada ta tona mata asiri
  • Matashiyar ta kara da cewar mijin yayar tata ya yi mata alkawarin tafiya turai bayan ta kama shi yana cin amana shima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa 'yar shekaru 18 wacce ba a bayyana sunanta ba, tana neman shawarar jama'a kan wasu ma'aurata da suka bata toshiyar baki bayan ta kama su suna cin amanar junansu.

Bisa ga wani sakon sirri da aka tura, wanda shafin @Wizarab10 ya wallafa, matashiyar ta ce yayarta da ke da aure ta bata naira miliyan 5 domin ta toshe mata baki bayan ta kama ta tana cin amana.

Kara karanta wannan

"Motata na da gado:" Matashiya za ta tuko mota daga Landan zuwa Legas, komai ya kammalu

Budurwa ta kama ma'aurata suna cin amanar junansu
An yi amfani da hoton don misali ne Hoto: Vladimir Vladimirov
Asali: Getty Images

Bayan shafe tsawon mako guda cikin tunani kan lamarin, ta yi yunkurin sanar da mijin yayar tata cin amanar da ta yi masa kawai sai ta kama shi da wata mata suna sharholiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiyar da ta shiga rudani ta yi ikirarin cewa mutumin ya yi alkawarin daukar nauyin karatunta a turai domin toshe mata baki. Sakonta na cewa:

"Na kama yar'uwata tana cin amanar mijinta sannan na karbi naira miliyan 5 a matsayin toshiyar baki amma na kasa bacci tsawon mako guda don haka na je sanar da mijinta abun da na gani a makon jiya.
"Na kama shi yana sharholiya da wata matar. A shirye yake ya tura ni karatu a UK. Shekaruna 18, shin na fadawa iyayena?"

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani kan ma'auratan da ke cin amana

Kara karanta wannan

"Ya hadu sosai": Matar aure ta cika da farin ciki yayin da mijinta ya wanke mata kayanta a bidiyo

@Anegbe_ ta ce:

"Labarin nan ba a bayyane yake ba, bayan kin karbi toshiyar baki daga yar'uwarki kina so ki fada ma mijinta, sai kika zo kika kama mijin sai kace a daki daya kuke zama."

@GorettiMojel

"Hajiya duk sun san abun da suke yi a wannan auren. Karbi kudin sannan ki bar wajen babu abun da ya shafe ki."
@GodwinLeo01
"Irin haka na faruwa idan magaji ya auri magajiya.
"Kowa na aikinsa a gefe daban-daban."

@JubrilZakariyau:

"Kina iya kama iyayenki a cikin irin wannan yanayi suma."

Matashiya za ta tuko mota daga Landan zuwa Legas

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya wacce ta 'dauki haramar tuki daga Landa zuwa Legas ta baje kolin cikin motarta.

Musamman aka shirya motar saboda wannan doguwar tafiya kasancewar tana dauke da yan abubuwa don jin dadin matashiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel