Sun Fi Na Buhari, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yi Wa Hafsoshin Tsaro, Ya Shawarci Mutane

Sun Fi Na Buhari, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yi Wa Hafsoshin Tsaro, Ya Shawarci Mutane

  • Yayin da matsalar tsaro ke kara kamari a Najeriya, Sanata Shehu Sani ya yi magana kan makomar hafsoshin tsaron kasar
  • Sanatan ya ce bai kamata tun yanzu a fara kiraye-kirayen sallamar su ba sai dai a kara ba su goyon baya don dakile matsalar
  • Sanatan ya bayyana haka ne a yau Talata 30 ga watan Janairu a shafinsa na X inda ya ce ya yi wuri a fara maganar korarsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi magana kan sallamar hafsoshin tsaron kasar.

Shehu ya na magana ne kan yadda matsalar tsaron musamman sace mutane da kashe-kashe ke kara kamari a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fara shirin murabus daga muƙaminsa don yin takara? Gaskiya ta bayyana

Shehu Sani ya yi magana kan matsalar tsaro
Shehu Sani ya bukaci goyon baya ga hafsoshin tsaro. Hoto: Shehu Sani.
Asali: Facebook

Mene Shehu Sani ke cewa kan tsaro?

Sani ya bukaci goyon bayan jama’a ga hafsoshin tsaron ba wai cin mutunci da kuma neman a sallame su ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hafsoshin tsaron sun sha suka musamman bayan kisan manyan sarakunan gargajiya da sace mutane a jihar Ekiti.

Sanatan ya bayyana haka ne a yau Talata 30 ga watan Janairu a shafinsa na X inda ya ce ya yi wuri a fara maganar korar hafsoshin tsaron.

Ya ce ko ba komai sun fi wadanda suka gabace su kokari a fannin tsaro duk da rikirkicewar matsalar, cewar Tribune.

Shawarin da ya bayar kan tsaro

A cewarsa:

“A wani wuri na karanta kirar wasu cewa a kori hafsoshin tsaro, bai kamata tun yanzu a kore su ba, akwai lalalcewar matsalar tsaro amma sun fi wadanda suka gabace su.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Ganduje ya tura sako mai muhimmanci game da alakarsa da su Kwankwaso

“Ya kamata a kara musu karfin gwiwa da kuma goyon baya don samar da tsaro a kasar baki daya.
“Matsalar tsaron da ake fama da ita yanzu sakamakon sakacin da aka samu ne a baya.”

‘Yan biniga sun hallaka sarakuna 2

Kun ji cewa wasu mahara sun hallaka manyan sarakunan gargajiya ajin farko guda biyu a jihar Ekiti.

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 29 ga watan Janairu yayin da sarakunan ke dawowa daga wata ganawar tsaro.

Maharan sun kai farmakin ne kan sarakunan guda uku inda daya daga cikinsu ya yi nasarar tserewa yayin da suka hallaka biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel