Alamomi guda 20 na Cutar Cancer da ya kamata kowa ya sani

Alamomi guda 20 na Cutar Cancer da ya kamata kowa ya sani

- Alamomin kansa-shin kai ko wani naka yana dauke da ita ga cikakkun bayanai akan kansa Wanda ya hada da hatsarin ta, alamomin kamuwa da ita duk zaka same su anan.

Alamomi guda 20 na ciwon Cancer da ya kamata kowa ya sani
Alamomi guda 20 na ciwon Cancer da ya kamata kowa ya sani

Alamomin kansa-shin kai ko wani naka yana dauke da ita ga cikakkun bayanai akan kansa Wanda ya hada da hatsarin ta, alamomin kamuwa da ita duk zaka same su anan.

MECECE CANCER?

Cancer tana iya kama ko wane bangare na jikin dan adam hakan yana faruwa idan jinin wurin ya gaza aikin sa, hakan yakan janyowa jiki ya kasa aikin daya kamata. ita cancer akan iya maganin ta, domin kuwa anyi wa mutane da yawa sannan sunci gaba da rayuwar su kamar sauran jama'a. zamu baku cikakken bayani akan cancer da kuma yanda ake maganin ta. zaku samu cikakken Bayani akan cancer da kuma ma'anar ta a karshen wannan rahoto.

ASALIN CANCER

Cancer bawai cuta ce guda daya ba ta rabu kala kala. Cancer takan iya farawa daga hunhu, nono, ciwo ko kuma ta jini. Cancer takan iya kamuwa ta gurare da dama amma kuma hanyoyin yaduwarta sun banbanta.

TAYAYA CANCER KE FARAWA?

Ko wace kwayar halitta ta jikin mu akwai aikin da takeyi ita asalin kwayar halittar takan kasu kashi kashi suna mutuwa idan aka fitar dasu ko kuma suka lalace sai wata kwayar ta maye gurbinsu a irin wannan lokaci ne cancer ke samun gurin zama ta zuba tata kwayar halittar ta kori asalin kwayar halitta.Wannan yana janyo matsaloli a sassan jikin da cancer ta kama.

Kwayar cutar kansa takan watsu a sauran sassan jiki. Misali kansar hunhu takan tafi cikin kasusuwa ta girma. A yayin da kwayar cancer ta yadu ana kiranta (meh-TAS-tuh-sis) ita kuma cancer hunhu idan ta tafi cikin kasusuwa ana kiranta (Lung Cancer) a turance. A bangaren likitoci kwayar cancer data shiga cikin kashi daidai take data hunhu sai dai idan ta yadu a cikin kashin.

BANBANCE BANBACEN CANCER?

Wata cancer din taka yadu cikin gaggawa yayin da wata take yaduwa a hankali kowacce akanyi maganinta ta hanya daban. Wata cancer din ta hanyar yin tiyata ne kadai za'a samu waraka. Wadda za'a sha magani ana kiranta chemotherapy (key-mo-THER-up-pee) a turance.

Idan mutum yana dauke da kansa likita yakanyi kokari wajen gano wace irin cancer yake dauke da ita. Mutanen dake da cancer anayi musu magani ne gwargwadon irin cancer da suke dauke da ita.

WANE MATSAYI CANCER TA TAKA?

Idan kana dauke da kansa likita zaiso sanin matakin da takai daga inda ta fara ana kiran sa "Cancer Stage" a turance zakaji mutane suna cewa cancer dinsu tana stage 1 ko stage 2. Sannan matsayin cancer dinka shi zai taimaka wajen sanin maganin da za'a doraka akai.

Kowace irin Cancer akwai gwajin da akeyi domin gane matasayin da ta kai. A dokar gwajin mataki na cancer mataki na 1 da mataki na 2 yana nufin cancer bata yi karfi sosai ba. Mataki na 3 da mataki na 4 kuma ta yadu sosai. Mataki na 4 shine makura wajen yaduwar ta.

DUBA WANNAN: Za a dakatar da Daliban da aka kama da laifin satar jarrabawa na tsawon shekaru

ALAMOMI GUDA 20 NA CANCER.

 1. Shashsheka/karancin numfashi.
 2. Tari da ciwon kirji alamace ta cancer hunhu ko na bargo. Ciwon kirjin yakan kasance daga kirjin zuwa kafada sannan ya sauko zuwa hannu.
 3. Zazzabi da saurin kamuwa da ciwo wannan ana kiranta Leukemia a turance hakan yana faruwa ne dalilin asalin kwayar halittar jinin mutum ta tabu.
 4. Fama wajen hadiye abu. Wannan yana nuni da an kamu da Easopageal cancer ko kuma Lung Cancer a turance.
 5. Futowar kurji me ruwa a wuya, hammata da gwiwa.
 6. Yawan zubda jini.
 7. Kasala da yawan gajiya
 8. Kumburin ciki
 9. Rashin sha'awar abu da kuma daukewar dandano.
 10. Ciwon ciki da Mara.
 11. Fitar jini daga dubura
 12. Rama ta lokaci guda.
 13. Yawan ciwon ciki
 14. Nono yayi ja ya kumbura alamace ta breast cancer.
 15. Canjawar kan nono.
 16. Nauyi da kuma ciwo na fitar hankali a lokacin al'ada wannan alama ce ta uterus cancer ana bukatar yin hoto (transviginal)
 17. Kumburin fuska.
 18. Canjawar farce zai iya kasancewa lung cancer idan kuma ya kode yayi fari to liver cancer ne.
 19. Ciwo baya a bangaren dama yana nuni da liver cancer ko breast cancer.
 20. Fesowar kuraje a jikin mutum

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel