Binciken El-Rufa’i: Majalisar Jihar Kaduna Ta Gurfanar da Mutanen Tsohon Gwamna

Binciken El-Rufa’i: Majalisar Jihar Kaduna Ta Gurfanar da Mutanen Tsohon Gwamna

  • Majalisar dokokin jihar Kaduna ta fara gurfanar da jami'an gwamnati domin binciken harkokin kudi lokacin Nasir El-Rufai
  • Jami'an gwamnati sama da biyar ne da suka yi aiki da Malam El-Rufai suka bayyana a gaban majalisar a ranar Litinin
  • Har ila yau, shugaban kwamitin binciken, Henry Danjuma ya yi karin haske kan yadda bincike yake gudana a jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Majalisar dokokin jihar Kaduna ta gurfanar da tsofaffin jami'an gwamnati domin cigaba da binciken tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Nasir ElRufa'i
Majalisar Kaduna ta gurfanar da jami'an gwamnatin El-Rufa'i domin bincike. Hoto: @SurajBamalli
Asali: Twitter

A ranar Litinin ne majalisar ta gayyato tsofaffin kwamishinoni, jami'an gudanarwa da 'yan kwangila domin yi musu tambayoyi.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gayyaci kamfanonin siminti domin amsa tambayoyi kan tashin farashi

El-Rufai: Wadanda majalisar ta gayyata

Jaridar Punch ta ruwaito cewa cikin wadanda aka gayyata sun hada da tsohon kwamishinan ayyuka, Thomas Gyang, tsohon kwamishinan ilimi Ja'afaru Ibrahim Sani da tsohon kwamishinan noma, Dr. Manzo Daniel Maigari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau sauran sun hada da shugaban gudanarwar gundumar Zariya, Balarabe Aliyu, shugaban gudanarwar Ƙafancan, Phoebe Yayi Sukai, shugaban kula da hanyoyin Kaduna, Muhammad Lawal Magaji.

Majalisar ta tabbatar da cewa binciken zai shafi dukkan harakokin kudi da aka yi a lokacin gwamna El-Rufai daga 2015 zuwa 2023.

Dalilin fara binciken gwamnatin El-Rufai

Binciken kuma yana zuwa ne biyo bayan kokawa da gwamnan jihar, Uba Sani ya yi kan bashin da ya yiwa Kaduna katutu.

Gwamna Uba Sani ya ce a halin da ake ciki na tarin bashi, da kyar yake biyan albashi.

Kara karanta wannan

"Babu laifin Tinubu": Mataimakin kakakin majalisa ya magantu kan matsin tattali

Rahotanni sun tabbatar da cewa majalisar ta binciki wasu jami'an gwamnatin Uba Sani domin fadada binciken.

Jawabain shugaban kwamitin binciken

Shugaban kwamitin binciken, Henry Danjuma ya ce za su binciki jami'an da suka yi aiki da El-Rufai da wadanda suke aiki da Uba Sani a halin yanzu.

A cewar shugaban, hakan zai taimakawa kwamitin wurin gano hakikanin halin da ake ciki game da lamarin.

Majalisa ta fara binciken zamanin El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta fara binciken tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, a kan mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.

Majalisar ta lissafa abubuwan da suka shafi harkokin kudi da binciken zai shafa tare da kafa kwamitin wucin gadi da zai yi aikin a kan lokaci

Asali: Legit.ng

Online view pixel