Rikicin Siyasar Kano: Ganduje Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Game da Alakarsa da Su Kwankwaso

Rikicin Siyasar Kano: Ganduje Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Game da Alakarsa da Su Kwankwaso

  • Shugaban APC na kasa, Ganduje ya bayyana kadan daga shirinsa na sanya siyasar kasar nan ta dauki saiti
  • Ganduje ya ce, zai hada kai da kowa don kawo karshen siyasar gaba a kasar nan muddin yana shugaban APC
  • Ana kyautata zaton Ganduje ya samu umarni daga Tinubu don tabbatar da ya yi sulhu da Kwankwaso nan kusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana aniyarsa ta kawo karshen siyasar gaba a kasar nan.

Ya bayyana cewa, hakan ne ma ya sanya ya fara yunkurin kawo sulhu tsakaninsa da tsohon mai gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

An hango Tinubu yana kallon yadda aka rantsar da sabon gwamnan Kogi daga Faransa, hotuna sun bayyana

Manufar Ganduje ya hada kan 'yan siyasa
Ganduje ya kudiri aniyar hada kan 'yan siyasa | Hoto: @Imranmuhdz, @KwankwasoRM
Asali: Twitter

sohon gwamnan na Kano dai ba ya jituwa da dan uwansa tsohon gwamnan Kano, inda suke da ra’ayin siyasa mai bambanci a tsawon lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje na son hada kan ‘yan siyasa

A cikin wata sanarwa da Ganduje ya fitar ta hannun hadiminsa a harkar yada labarai, Cif Oliver Okpala a ranar Lahadi, ya ce zai ci gaba da kokarin hada kan ‘yan siyasa a Najeriya.

A cewarsa, yana hakan ne don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da jituwa da juna a tsakanin ‘yan siyasar kasar nan, Daily Trust ta ruwaito

Idan baku manta ba, Kwankwaso ya bar APC ne tare da komawa PDP bayan samun sabani da Ganduje, inda daga baya ya koma NNPP tare da tsayawa takara a zaben 2023.

Tsananin gaba tsakanin Ganduje da Kwankwaso

Gaba tsakaninsu dai ta yi tsami a baya, wadda ta kai har aka hana Kwankwaso shiga jihar Kano a lokacin da Ganduje ke mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Bayan Sarkin Kano ya yi magana, Lauyoyi Musulmai sun yi babban abu 1 kan sace yaran Arewa zuwa Kudu

Amma daga baya, wasu rahotanni masu kura sun bayyana cewa, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci Ganduje da ya yi sulhu da Kwankwaso.

Kwanakin baya Ganduje ya kira Kwankwaso da sauran shugabannin NNPP na Kano ciki har da gwamna Abba Kabir Yusuf da su shigo inuwar APC.

Sai dai, mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya ce ba a gayyaci Yusuf a hukumance ba, saboda ya ga hakan ne soshiyal midiya.

Shugabanka zan zama a APC, Ganduje ga Kwankwaso

A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tunatar da kowa musamman jagoran Kwankwasiya, Rabiu Musa Kwankwaso cewa da zarar sun shigo APC, shi zai zama shugabansu.

Ganduje, a jawabin da ya yi cikin wani bidiyo da ya yadu, ya jadada cewa idan dai maganar jam'iyyar APC ake yi, shine lamba daya kuma mutum mafi muhimmanci.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake hangen akwai yiwuwar Ganduje ya hade da sauran mabiya Kwankwaso a inuwar APC mai mulkin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel