CBN: Duk da Ana ta Surutu, Ma’aikata 1500 da ke Abuja Za Su Fara Aiki a Legas

CBN: Duk da Ana ta Surutu, Ma’aikata 1500 da ke Abuja Za Su Fara Aiki a Legas

  • Duk da koke-koken da mutane suke yi musamman daga Arewa, ma’aikatan CBN sai sun bar Abuja
  • Ana maida wasu ma’aikatan bankin na CBN 1, 500 zuwa Legas kamar dai yadda aka shirya za ayi
  • Wasu da aka canzawa wurin aiki sun hakura, sun tattara kayansu daga babban birnin tarayyar kasar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Alal akalla ma’aikata 1, 500 na babban bankin Najeriya watau CBN za su bar birnin tarayya na Abuja zuwa garin Legas.

A ranar Talata, Punch ta tabatar da cewa surutan da mutane suke yi ba zai canza matsayar da babban bankin ya dauka ba.

Bankin CBN
Bankin CBN a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wani babban jami’in bankin na CBN ya shaida cewa ma’aikatan da aka dauke daga Abuja za su soma aiki a Legas ranar Juma’ar nan.

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 17, 000 a Karkashin Buhari da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar tace hayaniyar da ake yi da zargin shugabannin CBN da kokarin nakasa yankin Arewa bai sa an hakura da wannan shiri ba.

“Kwarai, shirin yana nan har yanzu kuma zuwa 2 ga watan Fubrairu za su shiga ofis, wanda shi ne makon farko a watan gobe.”

- Wani a CBN

Kungiyar dattawan Arewa ta ji haushin wannan mataki da zai rage adadin ma’aikatan CBN da ke Abuja daga 4, 233 zuwa 2, 733.

Ma'aikata na komawa CBN a Legas

Rahoton yace wasu ma’aikata sun fara tattara kayansu tuni daga Abuja zuwa Legas.

Majiyar tace mafi yawan ma’aikatan da ke sashen kula da bankuna da bangaren biyan kudi sun rungumi kaddara, suna yin kaura.

Abin ya shafi bangaren kula da abokan hulda da sashen tsare-tsaren tattalin arziki.

CBN: Menene dalilin janye ofioshin Abuja?

Kara karanta wannan

Mai Gidan Layla Othman ya zabi aika mata sako gaban duniya ana tsakiyar runtsi

Bankin na CBN yace ba haka nan kurum ya yanke shawarar wasu ma’aikata su bar Abuja, akwai kwararan dalilai da suka jawo wannna.

Daga cikin dalilan da aka bada shi ne domin ganin babban bankin yayi aikinsa da kyau.

Har ila yau, ana kuka da cewa ginin bankin Abuja ya yi kadan har ya zama barazana ga lafiya, kuma ana bukatar ma’aikata daga ko ina.

"Mun san za a rina"

A wata hira da Legit tayi da Buba Galadima, yace sun fadawa talakawa manufofin Bola Tinubu a zaben 2023 amma aka goya masa baya.

Jigon na NNPP yace kunnen-kashin jama'a ya yi sanadiyyar dauke wasu ofisoshin CBN da hedikwatar FAAN daga Abuja zuwa Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel