Jajirtaccen Sanatan Arewa Ya Fadi Masu Kai Shugaban Kasa Su Baro Shi a Aso Villa

Jajirtaccen Sanatan Arewa Ya Fadi Masu Kai Shugaban Kasa Su Baro Shi a Aso Villa

  • Muhammad Ali Ndume bai goyi bayan a kinkimi wasu ofisoshin gwamnatin tarayya zuwa garin Legas ba
  • Sanatan na kudancin jihar Borno ya zargi wasu na kusa da shugaban kasa da ba shi gurguwar shawara
  • Ndume ya tunawa gwamnatin Bola Tinubu cewa ba za ta yiwu Legas ta zama kishiyar birnin tarayya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa, ya soki dauke wasu ofisoshin gwamnati daga Abuja.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya yi hira da tashar Channels a kan shirin maida wasu ofisoshin CBN da hedikwatar FAAN zuwa Legas.

Ndume
CBN, FAAN: Bola Tinubu da Ali Ndume Hoto: @AjuriNgelale, @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Babban ‘dan siyasar ya yi ikirarin wasu miyagun ‘yan siyasa suke fadawa Mai girma shugaban kasa karya wajen daukar matakin nan.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cece-kuce kan mayar da manyan ofisoshi Legas, Tinubu zai lula kasar Faransa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaran Legas a fadar Shugaba Tinubu

Ali Ndume bai iya kama sunan kowa ba amma ya zargi wasu da ya kira yaran Legas a kusa da madafan iko da yaudarar Bola Tinubu.

Sanatan yana ganin ba daidai ba ne hedikwatar FAAN ta sake komawa garin Legas ko a dauke wasu ofisoshin bankin CBN daga Abuja.

Ndume yace za a dawo da FAAN, CBN Abuja

“Yaran Legas dinnan masu tunani Legas ce kurum Najeriya suna yaudarar shi ne kawai kuma ba su ba shugaban kasa shawarar gaskiya.”
“Wadannan miyagun ‘yan siyasa da ke kusa da madafan iko suna kokarin yaudarar shugaban kasa kuma za mu fada masa (Tinubu)”
“Sannan Mai girma shugaban kasa zai dauki mataki. Ba alfarma suke yi wa shugaban kasa ba saboda yana da tasiri a siyasance.”

- Sanata Muhammad Ali Ndume

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi maganar ficewar Kwankwaso daga NNPP zuwa APC da takarar 2027

Sanata Ndume za su ankarar da Tinubu

Arise ta rahoto Ndume yace birnin tarayya guda kurum ake da ita kuma ita ce Abuja. Wannan ta ce matsayar manya da Sanatocin Arewa.

‘Dan majalisar yana tunanin idan an fadakar da shugaban kasa, zai sake shawara, ya bar wadannan ofisoshin gwamnati a birnin tarayya.

Idan CBN suka tare a Legas, Ndume yana mamakin ko za a dauke hedikwatocin ma’aikatun mai su koma yankin Neja-Delta kenan.

Shugaba Tinubu yace dadi yana gaba

A rahoton da muka fitar a baya, an ji Bola Tinubu yayi wa ‘yan Najeriya tanadi, yace saura kiris a ci moriyar irin tsare-tsaren da ya kawo.

Mai girma Tinubu yace dole ta sa ya dauki tsauraran matakai amma a cewarsa za a ga amfanin hakan nan ba da dadewa ba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel