Shettima Ya Bayyana Gaskiya Kan Shirin Gwamnatin Tinubu na Mayar da Manyan Ofisoshi Zuwa Legas

Shettima Ya Bayyana Gaskiya Kan Shirin Gwamnatin Tinubu na Mayar da Manyan Ofisoshi Zuwa Legas

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi tsokaci kan batun mayar da manyan hukumomi da cibiyoyin FG zuwa Legas
  • Shettima ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ko kaɗan ba ta da wani shiri domin yin hakan
  • Mataimakin shugaban ƙasan ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin Tinubu za ta yi duk mai yiwuwa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaryata ikirarin cewa gwamnatin tarayya na shirin mayar da wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya zuwa Legas.

Ya bayyana haka ne ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, a wajen taron tunawa da Ahmadu Bello na shekara-shekara karo na 10, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana abu 1 da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa

Shettima ya musanta batun mayar da CBN zuwa Legas
Shettima ya yi magana kan batun mayar da manyan hukumomin FG zuwa Legas Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

An dai gudanar da taron a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Asabar, 27 ga watan Janairun 2024, rahoton Leadership ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Babu ƙanshin gaskiya a cikin jita-jitar da ke cewa gwamnatin tarayya na shirin mayar da hukumomi da cibiyoyin gwamnati daga Abuja fiye da aiwatar da sauye-sauyen harkokin mulki da ba za su yi wa wani yanki na ƙasar nan illa ba.
"Ina sake maimaitawa, wannan gwamnatin (gwamnatin Tinubu) ba za ta yi wa wani yanki na ƙasar nan illa ba don fifita wani yankin."

Shettima ya shawari shugabanni da dattawa

Mataimakin Shugaban ya kuma yi kira da cewa:

"Ina so in yi amfani da wannan dandalin don yin kira ga shugabanni da dattawan da ke da alhaki a kansu da su guji ɗaukar mataki kan irin waɗannan jita-jita."

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Ƴan bindigan da suka sace shugaban PDP na jiha sun aiko da saƙo mai ɗaga hankali

Da ya koma kan batun tsaro, wanda shi ne babban jigon lakcar, Shettima ya tunatar da mahalarta taron cewa tabbatar da tsaron ƙasar nan shi ne abin da gwamnatin Tinibu ta sa a gaba.

A cewarsa:

"Duk dabarun da za su iya kawo ƙarshen munanan laifuka da rikice-rikice a tsakanin al'ummomi, wannan gwamnatin za ta yi amfani da su."

Batun Mayar da Birnin Tarayya Zuwa Legas

A wani labarin kuma,.kun ji cewa fadar gwamnatin tarayy ta fito ta yi magana kan batun mayar da babban birnin tarayya daga Abuja zuwa Legas.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai ya musanta wannan jita-jitar da ake yaɗa wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel