“Ba Zai Illata Yan Arewa Ba”: Jigon PDP Ya Magantu Kan Mayar da Manyan Ofisoshi Legas

“Ba Zai Illata Yan Arewa Ba”: Jigon PDP Ya Magantu Kan Mayar da Manyan Ofisoshi Legas

  • Babban bankin CBN ya sanar da shirin mayar da wasu sassansa zuwa jihar Legas, saboda cunkoso a hedikwatarsa da ke Abuja
  • Haka kuma, gwamnatin tarayya ta sanar da mayar da hedkwatar hukumar FAAN zuwa Legas daga babban birnin tarayya Abuja
  • Wannan al'amari ya haifar da cece-kuce musamman a tsakanin mutanen arewa, wadanda suka nuna kyamar hakan ta wasu kungiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Reno Omokri, jigon jam'iyyar PDP ya bayyana mayar da manyan ofisoshin CBN da hukumar FAAN Legas da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta yi ba zai illata arewa ta fuskar siyasa ko tattalin arziki ba.

Reno Omokri ya goyi bayan mayar da manyan ofisoshi Legas
“Ba Zai Illata Yan Arewa Ba”: Jigon PDP Ya Magantu Kan Mayar da Manyan Ofisoshi Legas Hoto: Reno Omokri, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Omokri ya goyi bayan sauyawa sassan CBN da hedkwatar FAAN wuri

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan fashewar wani abu a Abuja, ya tafka mummunar ɓarna

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, Omokri ya cemayar da sassan CBN da hedikwatar FAAN zuwa Legas "don ci gaban tattalin arzikin Najeriya ne".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya ce idan Najeriya ta gaza yanke hukunci na gaskiya, kasar "ba za ta iya shiga a dama da ita a tattalin arzikin duniya ba."

Ya bayyana cewa ana iya sadaukar da sauran cibiyoyi ga siyasa amma ba tattalin arziki da rundunar sojin kasar ba.

Reno ya lissafo abubuwan da ya kamata a magance

Dan siyasar ya kuma yi nuni ga cewar babban abun da ya kamata Najeriya musamman Arewa ta mayar da hankali a kai, shine yadda za a kawo karshen fashi da makai da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da Legas babban birnin Najeriya? Fadar shugaban kasa ta fayyace gaskiya

Ya kuma ce kamata ya yi a mayar da hankali wajen tabbatar da ganin cewar yan arewa basa siyan mai da tsada fiye da yan kudu. Sannan a rage yawan yaran da basa zuwa makatanta da mayar da yan gudun hijita garuruwansu.

Har ila yau ya jaddada cewar kudaden da ake tarawa a Legas ba iya jihar ake kashe su ba, suna ratsa ko'ina musamman ma arewa.

Daga karshe ya ce:

"Har yanzu fadar shugaban kasa a Abuja take. Majalisar dokokin tarayya na nan daram-dam a babban birnin tarayya. Kotun Koli na nan daram dam. Haka kuma ma'aikatar tsaro.
"Babu jiha ko birnin da za ta iya takara da babban birnin tarayya, Abuja. Sai dai kuma idan muka ki daukar matakan gaskiya, Najeriya ba za ta iya shiga a dama da ita a tattalin arzikin duniya ba."

FG ta karyata mayar da FCT Legas

A wani labarin, mun ji cewa Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara ta musamman kan harkokin labarai ya yi watsi da rade-radin cewa Shugaban kasar na son mayar da babban birnin tarayyar kasar zuwa Legas.

Onanuga ya ce rade-radin mayar da babban birnin tarayyar kasar Legas ya fara ne a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 daga bangaren abokan hamayyar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel