“7.5% Ya Yi Kadan”: Gwamnatin Tinubu Za Ta Ƙara Harajin VAT, a Canja Tsarin Raba Kudi

“7.5% Ya Yi Kadan”: Gwamnatin Tinubu Za Ta Ƙara Harajin VAT, a Canja Tsarin Raba Kudi

  • Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar kara kudin harajin VAT da take karba yayin da aka sayi kaya ko aka sayar daga 7.5% na yanzu
  • Kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sauye-sauyen haraji ya gabatar da wannan bukatar a ranar Laraba a Abuja
  • Kwamitin ya kuma nemi da a kara kason kudin VAT da ake ba kananan hukumomi da jihohi zuwa 90% tare da ba gwamnatin tarayya 10%

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sauye-sauyen haraji ya ce akwai bukatar a kara yawan kudin da ake karba na harajin VAT.

Gwamnati na duba yiwuwar kara kudin harajin VAT
Gwamnatin tarayya za ta canja tsarin raba kudin haraji da kuma kara kudin VAT. Hoto: Getty Images, @officialSKSM (X)
Asali: UGC

Watakila harajin VAT ya tashi

Kwamitin ya ba da shawarar sake waiwayar harajin 7.5% na yanzu da ake cajar abokan ciniki tare da neman a kara kudin domin daidaita tattalin arziki, rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ki daukar matsaya kan harajin tsaron yanar gizo, 'dan majalisa ya koka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a taron fayyace manufofi da tasirin binciken kwamitin, shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa za a sake duba tsarin raba kudaden shiga na VAT.

Sabon tsarin rabon kudin VAT

Jaridar Vanguard ta ruwaito Oyedele ya ce kwamitin ya bayar da shawarar kara kason kudin VAT da ake ba kananan hukumomi da jihohi zuwa 90% daga 85% na yanzu.

Bisa ga sashe na 40 na dokar harajin VAT, gwamnatin tarayya na samun 15% na kudaden harajin, jihohi suna karbar 50%, sannan kananan hukumomi suna karbar 35%.

“Muna ba da shawarar rage kason gwamnatin tarayya daga 15% zuwa 10%. A bar wa jihohi da kananan hukumomi 90%."

- Taiyo Oyedele

Ya bayyana cewa sabon tsarin rabon kudin harajin VAT yana ba da fifiko ga kananan hukumomi domin haraji ne da ake tattarawa a matakin jihohi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi watsa watsa da Gwamnatin Bola Tinubu saboda lafta harajin 0.5% a banki

Kara kudin harajin VAT daga 7.5%

Gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta kara kudin harajin VAT daga 5% zuwa 7.5% hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) take karba idan aka siyo kayayyaki da kuma sayar da su.

Kamar yadda rahoton jaridar The Guardian ya nuna, shugaban kwamitin ya nemi a kara kudin harajin la'akari da cewa jihohi da dama za su iya shiga fatara saboda karancin haraji.

A yayin da ya ce karin kudin harajin ba zai wani shafi kananan 'yan kasuwa ba, sai dai Oyedele ya ce dole ne manyan 'yan kasuwa da masu sayen kaya da yawa su biya karin kudin.

An bullo da harajin tsaron yanar gizo

Tun da fari, mun ruwaito maku cewa gwamnatin tarayya ta hannun babban bankin kasar (CBN) ta bullo da harajin tsaron yanar gizo.

CBN ya umarci bankuna da su rika cire 0.5% idan abokan huldarsu sun yi hada-hadar kudi, lamarin da ya jawo cece-kuce a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel