Tinubu Zai Mayar da Legas Babban Birnin Najeriya? Fadar Shugaban Kasa Ta Fayyace Gaskiya

Tinubu Zai Mayar da Legas Babban Birnin Najeriya? Fadar Shugaban Kasa Ta Fayyace Gaskiya

  • Fadar shugaban kasa ta karyata rahoton cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na shirin mayar da babban birnin tarayya zuwa Legas
  • Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa Tinubu shawara ta musamman kan harkokin labarai ya ce jita-jitan ya fara ne a lokacin zaben 2023
  • Onanuga ya kuma bayyana dalilin mayar da wasu ofisoshin CBN da hedkwatar hukamar FAAN Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fadar shugaban kasa, Abuja - Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara ta musamman kan harkokin labarai ya yi watsi da rade-radin cewa Shugaban kasar na son mayar da babban birnin tarayyar kasar zuwa Legas.

Onanuga ya ce rade-radin mayar da babban birnin tarayyar kasar Legas ya fara ne a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 daga bangaren abokan hamayyar Tinubu.

Kara karanta wannan

Dara za ta ci gida yayin da shugaban EFCC ke fuskantar dauri a gidan kaso kan dalili 1 tak

Fadar shugaban kasa ta magantu kan dalilin dauke wasu ofisoshi zuwa Legas
Tinubu Zai Mayar da Legas Babban Birnin Najeriya? Fadar Shugaban Kasa Ta Fayyace Gaskiya Hoto: @aonanuga1956/@officialABAT
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa Abuja na nan daram-dam kasancewar doka ta goyi bayan ta zama babban birnin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @aonanuga1956, a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.

Dalilin mayar da CBN da FAAN Legas, Fadar shugaban kasa

Da yake magana kan mayar da CBN da FAAN zuwa Legas, ya ce magauta ne ke kokarin hada Arewa fada da Kudu.

Hadimin Tinubun ya ce dama can hukumar FAAN a Legas take kafin tsohon minista Hadi Sirika ya dauketa zuwa Abuja a lokacin mulkin Muhammadu Buhari.

"Bai kamata FAAN ta kasance a ko'ina sai dai kusa da masana’antar da take kula da shi. Har yanzu wasu bangarorin FAAN za su ci gaba da zama a Abuja, ba dauketa za a yi gaba daya ba.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cece-kuce kan mayar da manyan ofisoshi Legas, Tinubu zai lula kasar Faransa

“Hakazalika, bai kamata mayar da wasu bangarorin CBN zuwa Legas ya haifar da wani tashin hankali ba.
"Sassan da abin ya shafa, ciki har da sashin kula da bankuna, su ne wadanda ke hulda da bankunan kasuwanci, wadanda duk hedkwatarsu a Legas suke. Ya kamata mai gudanarwa ya kasance kusa da kasuwancin da yake kula da su."

Tinubu zai tafi birnin Faris

A wani labarin, mun ji cewa jirgin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai shilla birnin Faris, kasar Faransa.

Wannan ziyara da shugaban kasar zai kai kasar Faransan na gashin kai ne ba ziyarar aiki ba, kamar yadda rahoton ya nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel