Tinubu Zai Mayar da Babban Birnin Tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

Tinubu Zai Mayar da Babban Birnin Tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

  • Sanata Shehu Sani ya yi tsokaci kan rade-radin dauke babban birnin tarayyar Najeriya daga Abuja zuwa Legas
  • Tsohon dan majalisar dattawan ya ce mayar da babban birnin Najeriya wani wuri ba abu ne mai yiwuwa ba domin dai sai an bi tsarin kundin mulkin kasa
  • Ya bayyana cewa a baya, an siyasantar da lamarin dauke wasu hukumomin gwamnati saboda ra'ayin masu rike da madafun iko

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Ana tsaka da rade-radin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin dauke babban birnin tarayya daga Abuja zuwa Legas, Sanata Shehu Sani ya bayyana hgakan a matsayin babban aiki ja.

A cewar tsohon dan majalisar tarayyar, yin haka yana bukatar bin matakai na kudin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

Ku tuna cewa a kwanan ne gwamnatin tarayya ta mayar da hedkwatar hukumar FAAN da babban bankin kasar (CBN) zuwa Legas.

Shehu Sani ya ce abu ne mai wahala dauke birnin tarayya daga Abuja
Tinubu Zai Mayar da Babban Birnin Tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani Hoto: Shehu Sani/FCTA
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni wannan yunkuri ya haddasa cece-kuce daga bangarori daban-daban, inda wasu suka soki lamarin wasu kuma sun marawa matakin da shugaban kasar ya dauka baya.

A wata wallafa da ya yi a soshiyal midiya wanda Legit Hausa ta gani a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, Sanata Sani ya bayyana cewa:

“Kasancewar Abuja a matsayin babban birnin tarayyar Najeriya wani tanadi ne mai karfi a kundin tsarin mulki wanda babu wani mutum ko kungiya ciki har da shugaban kasa da zai iya canja sa.
"Matsayin Abuja na iya sauyawa ne idan aka yi wa kundin tsarin mulkin gyaran fuska, kuma sarkakiya da cece-kucen da ke tattare da sauya kundin tsarin mulkin kasar sananne ne.

Kara karanta wannan

"Ba zai illata arewa ba": Jigon PDP ya magantu kan mayar da manyan ofisoshi Legas

"Shugaba Tinubu ba zai iya dauke babban birnin Najeriya zuwa Legas ba, kuma na yarda cewa ba zai yi hakan ba. Amma ya kamata mu tunatar da kanmu cewa akwai hukumomin tarayya da basu da hedkwata a Abuja.
"Misali hedkwatar NECO a garin Minna take, BNTE na a Kaduna, NDDC a Port Harcourt, sannan hedkwatar hukumar jirgin kasan Najeriya na a Ebute Meta, Lagas."

Ra'ayin siyasa da dauke manyan ofisoshi

Sai dai kuma, ya bayyana cewa da gangan aka sanya wasu manyan ofisoshi a Abuja saboda ra'ayin siyasar shugabanni a baya.

Sanata Sani ya ce:

"...har yanzu wasu hukumomi na a wajen Abuja ne saboda ba a gina hedkwatarsu ba a Abuja."

Sai dai kuma ya bayyana cewa mutane na da damar fadin ra'ayinsu kan yiwuwar dauke babban birnin tarayyar kasar zuwa Legas amma ya bukaci yan majalisar tarayya da su fara tattauna batun don wayar da kai.

Dattawan arewa sun soki dauke manyan ofisoshi

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da Legas babban birnin Najeriya? Fadar shugaban kasa ta fayyace gaskiya

A baya mun ji cewa kungiyar ACF ta Dattawan Arewa ta soki shirin dauke hedikwatar hukumar FAAN daga birnin tarayya zuwa Legas.

Baya ga haka, jaridar Daily Trust ta ce kungiyar ba ta goyon bayan a dauke wasu manyan ofisoshin babban bankin CBN daga Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel