An Tsinci Gawar Budurwa a Dakin Otel Bayan Sun Je Holewa da Saurayinta, Yan Sanda Sun Dauki Mataki

An Tsinci Gawar Budurwa a Dakin Otel Bayan Sun Je Holewa da Saurayinta, Yan Sanda Sun Dauki Mataki

  • Wasu masoya biyu sun kwana a wani otel domin hutawa a unguwar Badagry da ke jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya
  • Daga baya ma'aikatan otel ɗin sun tarar da gawar budurwar da take tare da saurayinta a ɗakin da suka kama
  • Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da aukuwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Badagry, jihar Legas - An tsinci gawar wata mace a wani otel da ke Morogbo a yankin Badagry a jihar Legas.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a ranar Alhamis, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 31 ga watan Nuwamba.

An tsinci gawar budurwa a otel
An tsinci gawar wata budurwa a wani dakin otel a Legas Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ba a san inda saurayinta yake ba

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka yi wa jami'an NDLEA kwanton bauna, bidiyo ya bayyana

Marigayiyar dai tare da wani namiji dai sun sauka a otal ɗin da ke a jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan wasu ƴan sa'o'i, wani daga cikin ma'aikatan otel ɗin da yake shirin bayar da ɗakin ga wani daban, ya je ya tarar da ɗakin a kulle.

Daga baya ma’aikacin otal ɗin ya yi amfani da wani makulli domin buɗe ƙofar kuma daga baya ya tarar da budurwar a kwance a kan gado ba ta motsi.

An ce an ɗauke wayar marigayiyar. Duk ƙoƙarin gano saurayin ya ci tura domin ma'aikacin otel ɗin bai ɗauki bayanansu ba lokacin da suka zo otel ɗin, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

A halin da ake ciki, Benjamin Hundeyin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A kalamansa:

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ɗan kwallon Najeriya Musulmi ya yanke jiki ya faɗi a filin atisaye, Allah ya masa rasuwa

"An ajiye gawar a dakin ajiyar gawa. An kama mai otal ɗin tare da ma'aikacin."

An Yi Kaciɓus Da Gawar Budurwa a Otel

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tsinci gawar wata matashiya mai shekaru 28 a wani dakin otel da ke unguwar 102 Yale Okeowo, hanyar cikin gari, Ago Palace Way, jihar Lagas.

Lamarin ya auku ne a lokacin da wani matashi ya kama ɗaƙi a otel ɗin tare da budurwar. Bayan wasu ƴan mintoci, sai ya bar budurwar a cikin ɗakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel