Bayan Kara Kudin Wuta, Wani Mutumi Ya Sha Lantarkin Naira Miliyan 47 a Wata 1 a Abuja

Bayan Kara Kudin Wuta, Wani Mutumi Ya Sha Lantarkin Naira Miliyan 47 a Wata 1 a Abuja

  • Mohammed Jameel ya taba ikirarin akwai mutumin da ya sani da yake shan lantarkin sama da N14m a wata
  • Ganin an amince da karin kudi ga ‘yan sahun Band A, wannan bawan Allah ya ce mutumin nan zai sha wutan N40m
  • Ai kuwa hakan aka yi, a karshen watan Afrilu sai ga shi kamfanin AEDC ya kawo masa takarda zai biya N47m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mohammed Jameel wanda aka fi sani da White Nigerian ya bayyana yadda mutane suke shan wutar lantarki.

White Nigerian ya kawo labarin da wanda bai gani ba zai iya cewa karya ake yi, sai dai takardun kamfani za su gaskata shi.

Wutar lantarki
Wani ya sha wutar lantarkin N47m a Abuja Hoto: Getty Images/www.icirnigeria.org
Asali: UGC

A farkon watan Afrilun 2024 Mohammed Jameel ya ce akwai wani wanda ya sani da yake shan wutan N14m kowane wata.

Kara karanta wannan

Emefiele: “Yadda na biya cin hancin $600, 000 domin a biya ni kudin kwangila a CBN”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da gwamnatin tarayya ta cire tallafi kan 'yan sahun farko wajen shan wutar lantarki, kowace megawatta ta koma N220.

"Na san wanda yake biyan kamfanin @aedcelectricity N14m a duk wata a yanzu."
"Yayin da aka yi wannan karin (kudin shan wutar lantarki) ana nufin za su bukaci N40m a wata."
"Hukumar @NERC ku fada mana yadda masu otel, shaguna da sauran ‘yan kasuwa za su zauna da kafafunsu."

- White Nigerian

An shan kudin wutar lantarkin N47m

Bayan makonni sai ga shi kamfanin AEDC ya kawowa mutumin nan takardar biyan kudin wutan da ya sha a cikin watan Afrilu.

A lissafin da aka yi, wannan mutumi wanda ba a san shi ba, zai biya N47, 320, 287.42.

Tuni masu amfani da dandalin X suka fara tofa albarkacin bakinsu, har da masu ganin ba za ta yiwu a sha wutan miliyoyi haka ba.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Soki Shirin Tinubu Na Kashe Naira Tiriliyan 20 da Aka Ajiyewa ‘Yan Fansho

Martanin jama'a bayan ganin kudin wuta

A fege guda kuwa irinsu Duke of Africa sun yi wa White Nigerian gatse, ganin yadda ya ke goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.

Kwanakin baya an taba ji Jameel yana koda Bola Tinubu, har ya ce kyau mutane su karanci ilmin siyasa wajen shugaban kasar.

Captain Tango ya ce ko a otel ba a shan wutan Naira miliyan 14 a Najeriya.

Matasan da suka zama gwamnoni

A lokacin da aka dawo jamhuriyya ta hudu, an samu matasa da suka tsaya takarar gwamna, kuma suka samu muli a jihohinsu.

Akwai ‘yan kasa da shekaru 40 da su kayi mulki. Za a dade ana tunawa da irinsu Ahmad Sani Yariman-Bakura da Donald Duke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel