Kwankwaso, Matawalle da sauran tsaffin gwamnoni 13 da EFCC ta sake waiwayar zargin badakala kansu

Kwankwaso, Matawalle da sauran tsaffin gwamnoni 13 da EFCC ta sake waiwayar zargin badakala kansu

  • Akwai ‘yan siyasan da suka yi gwamnoni a jihohinsu da ake zargi da laifin taba baitul-mali
  • Hukumar EFCC tana binciken wasu daga cikinsu, akwai yiwuwar nan gaba kadan a koma kotu
  • Wannan jeri ba daga ofishin EFCC ya fito ba, an tattaro jerin wasu binciken da ke kasa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta sake dawo da binciken da ake yi wa wasu tsofaffin gwamnonin jihohi a Najeriya.

Binciken ya shafi tsofaffin gwamnoni 13 da kuma wasu wadanda suka rike mukaman ministoci kamar yadda Punch ta rahoto.

EFCC.
Shugaban EFCC da Bola Tinubu Hoto: @kc_journalist
Asali: Twitter

EFCC: An taba kudin jihohi da ma'aikatu

Zargin rashin gaskiya da ke kan wadannan manya ya kai N853.8bn. Ana tunanin an yi gaba da N772.2bn daga asusun jihohin kawai.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamna kan wani laifin da ya aikata lokacin yana ofis

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin ragowar N81.6bn da EFCC ta ke bincike sun yi kafa ne daga ma’aikatar jin kai da yaki da talauci a karkashin ministoci biyu.

Watakila EFCC ta binciki kudin makamai

Akwai wasu $2.2bn da ake zargin sun bace ta hanyar wawura a lokacin da Sambo Dasuki yake ba shugaban kasa shawara a kan tsaro.

An fitar da dalolin da sunan sayen makamai, amma aka karkatar da su. Binciken da kwamiti ya yi ya jefa 'yan siyasa da sojoji a matsala

Jerin tsofaffin gwamnonin da ake zargi da laifi a EFCC

1. Bello Matawalle – N70bn

2. Kayode Fayemi – N4bn

3. Ayo Fayose – N9.6bn

4. Ken Nnamani – N5.3bn

5. Sullivan Chime – N450m

6. Abdullahi Adamu – N15bn

7. Rabiu Kwakwanso – N10bn

8. Theodore Orji – N100bn

9. Danjuma Goje – N5bn

10. Aliyu Wammako – N15bn

11. Timipre Sylva – N19.2bn

Kara karanta wannan

Zargin cin hanci: EFCC za ta binciki ‘dan siyasar da ya fi kowa dadewa a majalisa

12. Sule Lamido – N1.2bn

13. Peter Odili – N100bn

Manyan binciken da ke gaban EFCC

Tun 2008, Peter Odili ya shigar da kara a kotu domin hana gwamnati ta bincike zargin abubuwan da ya daikata a lokacin yana ofis.

Zargin da ke kan Kwankwaso shi ne karkatar da kudin fansho sai ake zargin Chime da karbar kudi a hannun Diezani Alison-Madueke.

Matawalle da hukumar EFCC

Ana da labarin zargin da ake yi wa tsohon gwamnan Zamfara watau Bello Matawalle wanda yanzu karamin ministan tsaro ne na kasa.

Sabon shugaban EFCC, Olu Olukayode ya ce zai kakkabe takardun binciken jim kadan bayan Matawalle ya rasa kararsa a kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel