Alamomin da mai juna biyu za ta gane mace ko namiji take dauke da shi ba tare da gwaji ba

Alamomin da mai juna biyu za ta gane mace ko namiji take dauke da shi ba tare da gwaji ba

Daga cikin irin cigaban da ilimin kimiyya da fasaha ya zo da shi, akwai ilimin sarrafa na'urori domin warware kalubale na rayuwa, musamman kalubalen lafiya.

Daga cikin irin na'urorin da ake amfani da su a asibitocinmu, akwai na'urar da ake amfani da ita wajen gano abinda mace mai juna biyu ke dauke da shi; mace ko namiji.

Sai dai, tun kafin zuwan irin wadannan na'urori, akwai ilimin gargajiya da jama'a ke amfani da shi wajen hasashen abinda mai juna biyu ke dauke da shi a cikinta.

Ga wasu alamomi da ake amfani da su wajen hasashen abinda mai juna biyu ke dauke da shi a gargajiyance

1- ldan bangaren dama na ciki ya fi nauyi, alama ce dake nuna cewar namiji ne.

2- Idan jikin mai juna biyu ya fiye kyau mai kayatar wa, alama ce dake nuna namiji ne a cikin.

Alamomin da mai juna biyu za ta gane mace ko namiji take dauke da shi ba tare da gwaji ba
Alamomin da mai juna biyu za ta gane mace ko namiji take dauke da shi ba tare da gwaji ba
Asali: Depositphotos

3- Rashin motsin ciki sosai yayin juna biyu, shi ma alamar namiji ne.

4-ldan kan nonon ya yi ja sosai, alamar da namiji ne.

5- Yawan kasala yayin rainon ciki, alamar namji ne.

6 -Idan mai juna biyu ta na fara daga kafar dama in za ta yi tafiya, alama ce ta namiji ne a cikinta.

DUBA WANNAN: Jaruma Nafisa Abdullahi ta fitar da sabbin zafafan hotuna cikin sabon launi

7- Idan nonon bangaren dama ya fi na hagu girma yayin juna biyu, to namiji ne a cikin.

8- Idan kan nonon dama ya fi girma, shi ma haka.

9- Idan ya yi kewaye (fasalin kifa kwarya), alamar da namiji ce.

10- Fitar da madarar nonon mai kauri sosai, alama ce ta da namiji.

11- Idan idon mai ciki ya yi kalar ruwan dorawa, alamar da namiji ne.

12- Nuna wasu dabi‘u sabbi da mai juna biyu ba ta da su a baya, alama ce ta da namiji.

Duk wata alama da ta saba da wadanada aka lisafa a sama, to mace ce mai juna biyu ke dauke da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel