Betta Edu: Tsohuwar Shugaban Matan APC Da Wasu Abubuwan Sani Dangane Da Ministan Walwala Ta Tinubu

Betta Edu: Tsohuwar Shugaban Matan APC Da Wasu Abubuwan Sani Dangane Da Ministan Walwala Ta Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin 21 ga watan Agusta ya rantsar da Dakta Betta Edu da sauran ministocinsa domin zama cikakkun ministoci a Najeriya.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yin hakan ya sanya za su fara gudanar da ayyyuka a ma'aikatun da za su jagoranta.

Abubuwan sani dangane da Betta Edu
Betta Edu ita ce mafi ƙarancin shekaru a ministocin Tinubu Hoto: Dr Betta Edu Media Watch
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro wasu abubuwa da yakamata ku sani dangane da ministan walwala da yaƙi da talauci, Betta Edu.

1. Dakta Betta Edu ita ce mafi ƙarancin shekaru a ministocin Tinubu

An haifi Dakta Betta Edu a ranar 27 ga watan Oktoban 1986, wanda hakan ya sanya ta zama mafi ƙarancin shekaru da ta taɓa riƙe muƙamin minista a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Edu tsohuwar kwamishiniyar lafiya ce

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Ministocin Shari'a da Antoni Janar Na Tarayya da Aka Yi a Najeriya Tun Daga 1999

Dr Betta Edu tsohuwar kwamishiniyar lafiya ce a jihar Cross Rivers, muƙamin da ta riƙe tun daga shekarar 2019 har zuwa lokacin da ta yi murabus a shekarar 2022.

3. Betta Edu ta riƙe shugaban matan jam'iyyar APC

Betta Edu, ta riƙe muƙamim shugabar matan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta ƙasa, ita ce mafi ƙarancin shekaru da aka taɓa ba muƙamin.

Tana da shekara 36 a duniya lokacin da ta karɓi ragamar shugabancin matan jam'iyyar APC a watan Maris na shekarar 2022, cewar rahoton The Punch.

4. Edu kwararriyar likita ce

Edu tana da digiri a fannin aikin likitanci daga jami'ar Calabar, ta kuma yi karatu a jami'ar Harvard.

Edu ta nuna ƙwarewa da jajircewa a matsayinta na likita wajen ganin ta taimaki masu buƙata.

5. Edu ta samu karramawa

Haka kuma a watan Yulin 2023, gwamnatin tarayya ta hannun cibiyar bunƙasa cigaban mata ta Maryam Babangida tare da haɗin gwiwa da ma'aikatar harkokin mata, ta karrama Betta Edu da kyautar girmamawa kan shugabanci da kare haƙƙin mata.

Kara karanta wannan

Wahayi Daga Allah: Fitaccen Malami Ya Bayyana Wanda Zai Yi Nasara a Kotu Tsakanin Atiku da Peter Obi

Minista Ta Dukawa Shugaba Tinubu

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin ministocin da Shugaba Tinubu ya rantsar, da duƙa a gaban shugaban ƙasar.

Lola Ade-John sabuwar ministar yawon buɗe ido ta ɗuka a gaban shugaban ƙasar ne bayan an rantsar da ita, domin nuna farin cikinta kan wannan muƙami da ta samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel