Jerin wasu sabbin jami’ai da Buhari ya rantsar dasu manyan mukamai a hukamar NPC, da CCB

Jerin wasu sabbin jami’ai da Buhari ya rantsar dasu manyan mukamai a hukamar NPC, da CCB

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta ranar Laraba 7 ga watan Nuwamba daya gudana a babban dakin taro na fadar gwamnatin Najeriya, dake Aso Rock Villa.

Legit.com ta ruwaito ruwaito an samu halartar kusan kafatanin ministocin gwamnatin gaba daya zuwa taron da sauran manyan jami’an gwamnatin, daga cikinsu akwai Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

KU KARANTA: Wasu barayin mutane sun bayyana dalilin da yasa suka yi garkuwa da Uwardakinsu

Jerin wasu sabbin jami’ai da Buhari ya rantsar dasu manyan mukamai a hukamar NPC, da CCB
Buhari
Asali: Facebook

Daga cikin ministocin da suka halarta akwai Malam Adamu Adamu ministan ilimi, Ministan shari’a, Abubakar Malami, Ministan noma Audu Ogbeh, Karamin ministan noma Heineken Lokpobiri, Ministan kasafin kudi Udoma udo Udoma, Ministan wasanni Solomon Dalung, da Ministan karafa Bawa Bwari.

Sauran sun hada da Ministan sufuri Rotimi Amaechi, Ministan sufurin jirgin sama Hadi Sirika, Ministan ruwa Sulaiman Adamu, karamin ministan cinikayya Aisha Abubakar.

A yayin zaman na ranar Laraba, shugab Buhari ya rantsar da kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa, NPC, da hukumar ladabtar da ma’aikata, CCB, inda ya rantsar da Muhammed Isah daga jahar Jigawa a matsayin shugaban hukumar ladabtar da ma’aikata.

Jerin wasu sabbin jami’ai da Buhari ya rantsar dasu manyan mukamai a hukamar NPC, da CCB
Mutanen
Asali: UGC

Sauran kwamishinonin hukumar sun hada da Murtala Aliyu Kankia daga Katsina, Emmanuel Enu Attah daga Cross River, Ubolo Okpanachi daga Kogi, Ken Madaki Alkali daga Nasarawa, Farfesa S.F. Ogundare daga Oyo da Saad Abubakar daga Gombe.

Hakazalika shugaban kasa ya rantsar da mambobin hukumar kidaya da yawansu ya kai 23, daga cikinsu akwai Nwanne Johnny Nwabuisi daga Abia, Clifford Zirra daga Adamawa, Chidi Christopher Ezeoke daga Anambra, Isa Audu Buratai daga Borno, Charles Iyam Ogwa daga Cross River, Richard Odibo daga Delta, Okereke Darlington Onuabuchi daga Ebonyi da A.D. Olusegun Aiyajina daga Edo.

Sauran sun hada da Ejike Ezeh daga Enugu, Abubakar Mohammed Danburam daga Gombe, Farfesa Uba S.F. Nnabue daga Imo, Abdulmalik Mohammed Durunguwa daga Kaduna, Sulaiman Ismaila Lawal daga Kano, Farfesa Jimoh Habibat Isah daga Kogi, Sa’adu Ayinla Alanamu daga Kwara, Nasir Isa kwarra daga Nasarawa.

Sai kuma Aliyu Datti daga Niger, Yeye Seyi Adererinokun Olusanya daga Ogun, Prince Oladiran Garvey Iyantan daga Ondo, Mudashiru Oyetunde Hussain daga Osun, Cecilia Arsun Dapoet daga Plateau, Ipalibo Macdonald Harry daga Rivers, Sale S. Saany daga Taraba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel