Tinubu Ya Kira Wani Minista Zuwa Aso Villa Kan Badaƙalar N438m da Betta Edu, Bayanai Sun Fito

Tinubu Ya Kira Wani Minista Zuwa Aso Villa Kan Badaƙalar N438m da Betta Edu, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya kirawo ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, zuwa fadar shugaban ƙasa ranar Talata, 9 ga watan Janairu
  • Shugaban ƙasar ya bada wannan umarnin kiran ne biyo bayan zargin cewa Betta Edu ta bada wata kwangila ga kamfani mai alaƙa da Tunji Ojo
  • Tun da fari dai Mista Tunji-Ojo ya yi karin haske kan batun, inda ya ce ya yi murabus daga matsayin daraktan kamfanin bayan zaɓen 2019

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kirawo ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya je ya same shi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Wannan kira da Tinubu ya yi wa ministan na zuwa ne biyo bayan binciken da ake yi kan badaƙalar wasu kuɗaɗe a ma'aikatar jin kai da kuma wata kwangilar da aka bayar.

Kara karanta wannan

"Burin kowane ɗan Najeriya ya ɗauki hoto da ni" Ministan Tinubu ya yi magana mai jan hankali

Shugaba Tinubu da Tunji Ojo.
Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci ministan harkokin cikin gida Tunji-Ojo Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Tunji Ojo
Asali: Twitter

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ana zargin cewa ma'aikatar jin ƙai ta bada kwangilar kudi N438m ga kamfanin New Planet Projects Ltd, wanda ke da alaƙa Ministan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Tunji-Ojo ya fayyace gaskiya kan karɓan kwangila

Tun da farko, Ministan cikin gidan ya maida martani kan zargin da ake yaɗawa cewa kamfaninsa, New Planet Project Ltd, ya karɓi kwangila daga Betta Edu, dakatacciyar ministar jin ƙai.

A wata hira da Channels tv ranar Litinin, Tunji-Ojo ya bayyana cewa ya kafa kamfanin shekaru 15 da suka wuce amma ya yi murabus daga matsayin darakta bayan zaɓensa a 2019.

A cikin shirin, ministan ya gabatar da takardar CAC da ke nuna murabus dinsa a matsayin darakta na New Planet Project Limited shekaru biyar da suka gabata.

Kowa so yake ya ɗauki hoto da Wike - Ministan Abuja

Kara karanta wannan

Badaƙalar N37bn: Jami'an EFCC sun titsiye tsohuwar ministar Buhari, sun tashi muhimman bayanai

A wani rahoton na daban Ministan babban birnin tarayya Abuja ya yi ikirarin cewa kowane ɗan Najeriya na son ya ɗauki hoto da shi.

Nyesom Wike ya bayyana cewa duk da zagi da sukar da ake masa a kafafen sada zumunta, ba haka abun yake ba a fili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel