Na Tausaya Mata: Budurwa Ta Durkusa a Gaban Saurayinta a Kan Titi Don Neman Gafararsa

Na Tausaya Mata: Budurwa Ta Durkusa a Gaban Saurayinta a Kan Titi Don Neman Gafararsa

  • Wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya wanda ya nuno wata budurwa durkushe a gaban saurayinta a kan titi ya haddasa cece-kuce
  • A cikin bidiyon, mutumin na rike da jaka yayin da ya dauke ido daga kan matar wacce ke duke a kan gwiwoyinta
  • Bayan dan wani lokaci, sai ta karbi jakanta daga hannun mutumin, ta mike sannan ta kara gaba ta daya gefen

Jama'a sun yi cece-kuce kan wani bidiyo na wata budurwa yar Najeriya da ke duke a gaban saurayinta don rokonsa gafara.

Wani bidiyon ban takaici ya nuno ta a kan gwiwoyinta a gaban mutumin a kan titi, lamarin da ya sa mutane yin tambayoyi da cece-kuce.

Saurayi da budurwa
Na Tausaya Mata: Budurwa Ta Durkusa a Gaban Saurayinta a Kan Titi Don Neman Gafararsa Hoto: @lindaikejisblog
Asali: Instagram

A cikin bidiyon, an gano ta a durkushe yayin da wani ke daukarta bidiyo daga tsallaken wajen.

Tana ta wasu zantuka da ba ji sannan ta roki mutumin wanda ya nuna sam hankalinsa baya kanta.

Kara karanta wannan

Zabin Allah Na Bi: Bidiyon Soyayya Da Wata Kyakkyawar Mata Da Mijinta Mai Nakasa Ya Tsuma Zukata

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan yar diraman ya ja hankalin masu wucewa, koda dai babu wanda ya tsaya balle ya tsoma masu baki a lamarinsu.

Bayan dan wani lokaci, budurwar ta tashi tsaye sannan ta karbi jakar daga hannun mutumin, ta goge jikinta sannan ta yi tafiyarta ta daya bangaren. Har lokacin matashin na nan tsaye a inda yake.

Jama'a sun yi martani

@mseroticaa ta rubuta:

"A yan shekaru kadan masu zuwa, za ta tuna da wannan lokacin sannan ta ji kunya."

@umycutie a rubuta:

"Ya Ubangiji, wannan diya daya da nake da ita, kada ka bari ta aikata irin wannan abun. Mamarta bata yi ba dan Allah."

@queenofdsun ta ce:

"A kalla da ya ce mata ta tashi tsaye, ya yake ji a ransa kallonta a haka."

@monidreezy ta ce:

"Ban san me yasa nake taya ta jin ciwon abun ba. Ban yarda cewa wannan yar Najeriya bace...da ta kira Pablo ya zo da mota ya dauke ta."

Kara karanta wannan

Bidiyon Bidloniyan Najeriya Yana Rabawa Matasa $100 Kowannensu Ana Tsaka da Matsalar Kudi

@suzzyvulu ta yi martani:

"Ba girman kai bane amma ba zan taba iya yin wannan abun ba."

A wani labarin, wata mata da mijinta mai nakasa sun nunawa duniya cewa lallai har yanzu akwai soyayya ta gaskiya bayan sun saki bidiyonsu cike da shaukin juna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel