An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Addar Tsohon Gwamna a Najeriya, Bayanai Sun Fito

An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Addar Tsohon Gwamna a Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Addar tsohon gwamnan Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola ta rasu ta na da shekara 87 a duniya a yau Alhamis
  • Marigayiyar Victoria Moradehun Popoola ta kasance kamar uwa a wurin tsohon gwamnan bayan rasuwar mahaifiyarsa
  • Popoola wacce ungozoma ce ta yi ritaya kuma ta kasance babbar ƴa a cikin iyalan Oba Moses Oyinlola

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola ya rasa addarsa.

Marigayiyar Victoria Moradehun Popoola ta rasu ta na da shekaru 87 a duniya a yau Juma'a 29 ga watan Disamba.

Addar tsohon gwamna a Najeriya ta riga mu gidan gaskiya
An sanar da rasuwar yar uwar tsohon gwamnan jihar Osun, Oyinlola. Hoto: Prince Olagunsoye Oyinlola.
Asali: Facebook

Wace ce marigayiya Victoria a wurin Oyinlola?

Popoola wacce ungozoma ce da ta yi ritaya ita ce babbar ƴa a wurin mahaifiyarsa, cewar Tribune..

Kara karanta wannan

2024: Kwanaki 2 da mutuwar gwamna, Lucky ya manta da shi ya ziyarci Tinubu kan wani babban dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayiyar ta kasance uwa a wurin Oyinlola bayan rasuwar mahaifiyarsu a shekarar 1959 lokacin ya na shekara takwas.

Victoria ta yi aiki a jihar Sokoto lokacin da tsohon gwamnan ya shiga aikin soja a shekarar 1969.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan rasuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a kasar Jamus, cewar IRepoteronline.

Wane martani tsohon gwamnan ya yi kan rasuwar?

Tsohon gwamnan ya bayyana mutuwar marigayar a matsayin karshen iyalan Oba Moses Oyinlola.

Ya bayyana marigayar a matsayin uwa ta biyu a gare shi wacce ta dauki nauyin karatunsa da rayuwarsa tun ya na karami.

Daga cikin wadanda suka tura sakon ta'aziya akwai tsohon mataimakinsa, Erelu Olusola Obada inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

A cikin makon na da muke ciki an samu mace-macen manyan mutane masu mukami a Najeriya da dama.

Kara karanta wannan

Karin hadiman gwamna 2 sun yi murabus daga muƙamansu, sun bayyana babban dalili

Daga cikinsu akwai tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Ghali Na'Abba ya riga mu gidan gaskiya a Abuja

A wani labarin, da safiyar Laraba ce 27 ga watan Disamba aka wayi gari da rasuwar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba.

Na'Abba ya rasu a wani asibiti da ke birnin Tarayya, Abuja bayan fama da doguwar jinya.

Da yammacin ranar ce aka binne mamacin da misalin karfe 5:38 na yamma a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel