‘Yan Majalisa Sun Katse Hutu Domin Biyawa Bola Tinubu Bukatar Kasafin Kudin 2024

‘Yan Majalisa Sun Katse Hutu Domin Biyawa Bola Tinubu Bukatar Kasafin Kudin 2024

  • Opeyemi Micheal Bamidele ya ce Majalisar tarayya za ta amince da sabon kundi kafin shekarar nan ta kare
  • ‘Dan majalisar dattawan ya ce har ranakun Asabar su ka rika zama saboda kasafin kudin 2024 ya zama doka
  • Sanata Opeyemi Micheal Bamidele ya nuna za su koma aiki bayan takaita hutun kirismetin shekarar bana

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Micheal Bamidele, ya shaida cewa za a amince da kasafin kudin 2024.

Sanata Opeyemi Micheal Bamidele ya ce a ranar 30 ga watan Disamba za a amince da kundin kasafin kudin badi, Punch ta fitar da labarin.

Kasafin kudin 2024
Kasafin kudin 2024 a Majalisa Hoto: @officialsksm
Asali: Facebook

‘Dan majalisar dattawan ya tabbatar da haka ne a lokacin da manema labarai su ka tattauna da shi a Iyin-Ekiti a jihar Ekiti ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun yi bikin Kirsimeti ba tare da albashin Disamba ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Opeyemi Micheal Bamidele ya nuna ‘yan majalisar tarayya za su hakura hutunsu, su koma ofis saboda a kammala aiki kan kasafin kudin.

Aikin kasafin kudin 2024 a Majalisa

"Domin ganin an amince da kasafin kudin, mun takaita lokaci ga duka ma’aikata, hukumomi da cibiyoyin gwamnati su bayyana gaban kwamitocin da su ka dace a majalisar wakilai da dattawa.
Wannan ya rage rabin lokacin da ake tsaida wajen kare kasafin kudi a maimakon a bayyana gaban kwamitocin majalisar dattawa sai daga baya a koma gaban kwamitin majalisar wakilai.
Matakin nan ya kuma cire lokacin da ake batawa wajen daidaita aikin majalisun. A takaice dai mun yi nasarar rage bata lokaci."

- Opeyemi Micheal Bamidele

Yadda aka yi zama har ranakun hutu

Bayan haka, an rahoto Opeyemi Micheal Bamidele yana cewa sun rika yin zama har a ranakun da su aiki saboda a karkare aikin kasafin.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya ware naira biliyan 1.95 don sake gina fadar sarakunan gargajiya a Zamfara

Sanatan ya ce akwai yiwuwar har ranar Lahadi su zauna ganin karshen shekara ta zo.

Hutun kwanaki uku kurum ‘yan majalisar suka samu da kirismetin nan duk domin ganin an iya fara amfani da kasafin kudin daga Junairu.

Tsohon shugaban majalisa ya rasu

A yau aka wayi gari da labari cewa Ghali Umar Na’Abba wanda ya shugabanci majalisar wakilan tarayya daga 1999 zuwa 2003 ya rasu.

Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba ya cika ne a gidansa a Abuja bayan ya yi ‘yar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel