Tinubu Ya Sallami Wanda Buhari Ya Naɗa, Ya Maye Gurbinsa da Yaron Wike

Tinubu Ya Sallami Wanda Buhari Ya Naɗa, Ya Maye Gurbinsa da Yaron Wike

  • Shugaba Bola Tinubu ya kori wanda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada tare da maye gurbinsa
  • Tinubu ya nada Injinya Chukwuemeka Woke a matsayin babban daraktan hukumar Ogun-Osun River Basin a Najeriya
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar a jiya Alhamis 9 ga watan Mayu a Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada Injinya Chukwuemeka Woke babban daraktan hukumar Ogun-Osun River Basin.

Woke babban amini ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda ya ba shi shugaban ma'aikatansa lokacin mulkinsa a jihar Rivers.

Tinubu ya naɗa na hannun daman Wike bayan korar wanda Buhari ya ba muƙami
Bola Tinubu ya kori wanda Muhammadu Buhari ya nada muƙami yayin da ya ba yaron Nyesom Wike. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Tinubu ya nada yaron Wike muƙami

Kara karanta wannan

Duk da kokarin Tinubu, Rikicin Wike da Fubara ya sake munana bayan matakin Majalisa

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a jiya Alhamis 9 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Woke ya maye gurbin Olufemi Odumosu wanda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada a 2021 bayan dawowarsa mulki a wa'adi na biyu.

"Woke kwararren Injiniya ne kuma ɗan siyasa, ya mulki karamar hukumar Emohua a jihar Rivers."
"Ya rike shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Rivers a lokacin mulkin tsohon gwamna, Nyesom Wike na tsawon shekaru."
"Tinubu ya bukaci Woke ya yi aiki tukuru domin samar da ci gaba a bangaren albarkatun ruwa wurin yin aiki da gaskiya."

- Ajuri Ngelale

Tinubu ya jawo shi bayan rabuwa da Fubara

Har ila yau, Woke ya rike muƙamin kwamishinan ayyuka na musamman a gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Harajin CBN: Na hannun daman Tinubu ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi

Sai dai Woke yana daga cikin wadanda suka ajiye mukamansu a gwamnatin bayan an samu matsala tsakanin Wike da gwamna Fubara.

Sanata ya shawarci Tinubu kan wasu Ministoci

A wani labarin, Mamban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Dattawa, Jimoh Ibrahim, ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya kori wasu daga cikin ministocinsa.

Jimoh Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi kan majalisar ministoci da muƙarraban Tinubu yayin hira da 'yan jaridu.

Sanatan ya ce akwai wadanda suka cancanci a dakatar da su saboda rashin yin katabus a gwamnatin inda ya bukaci a maye gurbinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.