Fitaccen Jarumin Fina finai Ya Gabatar da Ɗansa a Fim, Ya Gargadi Jarumai da Ma'aikata

Fitaccen Jarumin Fina finai Ya Gabatar da Ɗansa a Fim, Ya Gargadi Jarumai da Ma'aikata

  • Jarumin fina-finai a masana'antar Nollywood, Kanayo O. Kanayo ya gabatar da babban ɗansa a kamfaninsa domin gudanar da fim
  • Kanayo ya ce ɗan cikinsa, Clinton Onyeze Mbaise zai kasance mai taimaka masa na musamman a harkar shirya fina-finai
  • Sai dai ya gargadi sauran wadanda suke aiki tare da kada su fifita shi a matsayin ɗansa inda ya ce zai biya shi kamar yadda ya ke biyan kowa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Kanayo O. Kanayo ya gabatar da babban ɗansa a harkar wasan kwaikwayo.

Kanayo ya gabatar da ɗansa mai suna Clinton Mbaise a masana'antar shirya fina-finai domin taimakawa masa a kamfaninsa.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

Jarumin fina-finai ya nada ɗan cikinsa mai bashi shawara a masana'antar
Fitaccen jarumin Kanayo O. Kanayo ya gabatar da ɗansa a masana'antar shirya fina-finai. Hoto: @kanayo.o.kanayo.
Asali: Instagram

Fim: Wane matsayi Kanayo ya ba ɗansa?

Jarumin ya ce Clinton zai zamo mai taimaka masa na musanman a shirya fina-finai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen jarumin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo a shafin Instagram inda ya bukaci kada a ba shi wani fifiko na musamman.

"Wannan shi ne Clinton Oyenze Mbaise, babban ɗan ciki na, zai yi aiki damu a wannan kamfani a matsayin mataimakina na musamman."
"Ka da ku fifita shi saboda ɗan cikina na ne, wannan gargadi ne ga dukkan kowa, zan biya shi kamar yadda ake biyan kowa."
"Ka da ku fara cewa wannan ɗan K.O.K ne, ba na son irin haka, ku dauke shi kamar sauran mutane da ke wannan masana'anta."

- Kanayo O. Kanayo

Mbaise ya karanci harkar fim a jami'a?

Kanayo ya ce Mbaise ya kammala digiri dinsa a Jami'ar Babcock a bangaren Fasahar Sadarwa ta Zamani.

Kara karanta wannan

" Za a gama titin Abuja-Kaduna-Katsina" Ministan Tinubu ya tsaida lokaci

Gwarzon ya ce Mbaise ya karanta bangaren shirya fina-finai da kuma gudanarwa kafin ci gaba da karatunsa.

Ali Nuhu ya magantu kan Adam Zango

A wani labarin, kun ji cewa Nuhu ya fito ya yi magana kan halin da jarumin masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya samu kansa a ciki.

Ali Nuhu wanda shi ne shugaban hukumar kula da fina-finai ta Najeriya, ya bayyana cewa Adam A. Zango na cikin ƙoshin lafiya.

Wannan na zuwa ne biyo bayan wallafar da fitaccen jarumin ya yi kan cewa yana cikin wani mawuyacin hali a rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel