Abuja da Nasarawa: An Ƙara Tona Asirin Waɗanda Ake Zargi da Cirewa Yara Ƙoda

Abuja da Nasarawa: An Ƙara Tona Asirin Waɗanda Ake Zargi da Cirewa Yara Ƙoda

  • Babbar kotun Abuja ta fara sauraron shaidu kan karar zargin cire sassan jikin ɗan adam ba bisa ka'ida ba a birnin tarayya da jihar Nasarawa
  • Wani dillalin wayoyin hannu ya bayyana cewa ɗaya daga cikin yaran da aka cire wa ƙoda a asibitin ya sayi babbar waya a wurinsa
  • Abdullahi Mohammed ya shaidawa kotun cewa yaron ya tura masa kuɗi N500,000 a asusu daga baya ya karɓi canjin N210,000

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da ake ci gaba da samun bayanai kan cirewa yara ƙoda ba kan ƙa'ida ba, hukumar yaƙi da safarar mutane NAPTIP ta fara gabatar da shaidu a gaban kotu.

Wani mai sayar da wayoyin hannu ya shaidawa babbar kotun Abuja cewa ɗaya daga cikin yaran da aka cire wa ƙoda ya sayi waya a hannunsa.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na shirin kafa jam'iyya domin lallasa Tinubu a 2027

Kotu ta fara sauraron shari'ar cire sassan jiki.
Shaida ya bayyana yadda yaron da aka cire wa ƙoda ya siya waya a wurinsa a Nasarawa Hoto: Federal High Court
Asali: Twitter

Ya saida koda ya saye wayar zamani

Abdullahi Mohammed, mai shagon sayar da wayoyi a Mararaba a jihar Nasarawa ya ce yaron ya zo shagonsa ya sayi babbar waya jim kaɗan bayan an cire masa ƙoda a wani asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya faɗi sunan yaron, Oluwatobi Salmon Adedoyin, inda ya bayyana cewa ya zo ya sayi waya ta N290,000 a shagonsa ranar 20 ga watan Fabrairu, 2023, Daily Trust ta rahoto.

Dillalin wayoyin ya yi wannan bayanin ne yayin da lauyan masu ƙara watau hukumar NAPTIP, Hassan Tahir Esq ya gabatar da shi a matsayin shaida ranar Alhamis.

Yadda ya sayi waya bayan cire koda

Shaidan ya ci gaba da cewa ya bai wa yaron bayanan asusun bankinsa kuma ba da jimawa ba aka turo masa kuɗi N500,000.

"Na tambaye shi meyasa ya ciko mun kuɗin, sai ya bani lambar asusun Opay domin na tura masa ragowar N210,000 kuma daga nan ya kama gabansa."

Kara karanta wannan

Tsohon minista Hadi Sirika ya kafa misali da annabawa yayin da ya gurfana a gaban kotu

Tun farko dai hukumar yaƙi da safarar mutane NAPTIP ta gurfanar da ma'aikata huɗu na asibitin Alliance Hospital and Service Ltd bisa zargin cire sassan jiki ba kan ƙa'ida ba.

Ma'aikatan da hukumar ta gurfanar bisa tuhume-tuhume 11 sun haɗa da, Dakta Christopher Otabor, Emmanuel Muyiwa Olorunlaye, Chikaodili Ugochukwu da Dokta Aremu Abayomi.

Jaridar ta fara fallasa yadda ake cinikin sassan jikin mutum a sassan Abuja da jihar Nasarawa bayan bincike da tattaunawa da wadanda abin ya shafa.

EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika

A wani rahoton na daban tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ɗiyarsa, Fatima Hadi Sirika, sun isa harabar babbar kotun tarayya.

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari'a kan yadda aka yi da wasu kuɗin kwangila N2.7bn a lokacin yana kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel