“Shugaba a Shekaru 20”: Yar Najeriya Ta Yi Tattalin Kudinta da Kyau, Ta Gina Haddaden Gidan Dinki

“Shugaba a Shekaru 20”: Yar Najeriya Ta Yi Tattalin Kudinta da Kyau, Ta Gina Haddaden Gidan Dinki

  • Wata budurwa yar Najeriya ta cika da farin ciki yayin da ta bude hadadden gidan dinki nata na kanta irin wanda take mafarki
  • Ta wallafa wani bidiyo a TikTok don nunawa mutane sakamakon aikin da ta yi da kuma tarin kayayyakin da ta siya
  • Ta sanar da mabiyanta cewa ta shafe tsawon wata guda kafin ta kammala aiki a gidan dinkin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta bayyana tsantsar farin cikinta yayin da ta yi nasarar kammala aikin gidan dinkinta.

Matashiyar mai suna 'Celebrities Tailor' a TikTok, ta bayyana cewa tana matukar farin ciki da ganin abubuwa sun kammalu a gidan dinkin.

Kara karanta wannan

Budurwa za ta yi wuff da abokin saurayinta, ta saki zafafan hotunan kafin aure

Budurwa ta gidan dinki
“Shugaba a Shekaru 20”: Yar Najeriya Ta Yi Tattalin Kudinta da Kyau, Ta Gina Haddaden Gidan Dinki Hoto: TikTok/@celebrities_tailor.
Asali: TikTok

Ta ce shekarunta 20 kacal a duniya, amma ta zama shugaba da kanta a lokacin da take ganiyar kuruciya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, ta shafe tsawon wata guda kafin kammala aiki a gidan dinkin.

An gano ta a bidiyon tana kawata wajen da labulaye da kuma jera sauran kayan aiki da wuraren da suka kamata.

Ta rubuta:

"Zan zaga da ku don ganin aikin wata daya cikin bidiyo mai tsawon minti daya. Lallai Allah mai girma ne. Ina taya kaina farin ciki."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Asa Ndi Oga ta ce:

"Kalli abun da sa'o'ina suke yi."

@Hebron Augusta ta ce:

"Kina da masu mara maki baya mana. Gani nan, amma ina gab da cimma mafarkina irin wannan."

@Abiola wear ta yi martani:

"Shekaruna 19. Zan cika 20 a shekara mai zuwa kuma nima mai dinki ce kuma ina so na zama shugaba nima a shekara mai zuwa."

Kara karanta wannan

"Ban iya bacci ba": Budurwa ta fashe da kuka bayan ta gano saurayinta na shekaru 3 ya yi aure

@ADETOUN ta ce:

"Kungiyar tailoli na gaishe ki."

@Young tailor ta ce:

"Zan cika shekaru 20 shekara mai zuwa ina fatan samun rahamar Allah."

@Expensivegift ta ce:

"Allah da ya yi maki ya yi mun nawa nima a shekara mai zuwa Amin."

Budurwa ta karbewa saurayi N20k

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutumi da ya turawa budurwa kudin N20,000 domin ta yi kudin motar zuwa ganinsa a Abuja ya nuna fushinsa saboda ta ki zuwa.

A wata wallafa da ta yi a TikTok, an jiyo muryar mnutumin yana kiran budurwar a matsayin yar 419.

Asali: Legit.ng

Online view pixel