“Ban Iya Bacci Ba”: Budurwa Ta Fashe da Kuka Bayan Ta Gano Saurayinta Na Shekaru 3 Ya Yi Aure

“Ban Iya Bacci Ba”: Budurwa Ta Fashe da Kuka Bayan Ta Gano Saurayinta Na Shekaru 3 Ya Yi Aure

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta fashe da kuka don nuna fushinta bayan ta samu labarin cewa saurayinta ya yi auren sirri
  • Matashiyar wacce ta karaya ta ce sun shafe tsawon shekaru uku suna soyayya kuma ta zata ita zai aura
  • Ta nuna kaduwa kan lamarin, inda ta ce lamarin ya sa ta kasa bacci tsawon shekaru biyu da suka gabata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata budurwa yar Najeriya ta koka yayin da ta sanar da cewar saurayinta na shekaru uku ya auri wata daban a kwanan nan.

Matashiyar, @sexysica_, ta magantu kan soyayyarsu a TikTok yayin da ta dungi zubar da hawaye.

Matashiya ta koka bayan saurayinta ya yi aure a boye
“Ban Iya Bacci Ba”: Budurwa Ta Fashe da Kuka Bayan Ta Gano Saurayinta Na Shekaru 3 Ya Yi Aure Hoto: @sexysica_.
Asali: TikTok

Ta ce a kodayaushe yana yi mata kashedi cewa kada ta daura hotonsa a shafinta, cewa shi ya fi sha'awar su yi soyayyarsu cikin sirri.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lalong ya magantu kan barin majalisar Tinubu ko komawa majalisar dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ashe sine dalilin da yasa kullun yake gargadina kan kada na yarda na daura shi a shafina cewa yana son soyayya ta sirri. Har yanzu ina kokarin shanye komai. Na rantse ba zan taba aika masa sako ko kiransa ba. Ba zan nemi jin ta bakinsa ba. Bana ma son jin yadda ko dalilin da yasa hakan ya faru. Ya yi abun da zai yi, na ji yadda zan ji, ya kasance yadda yake," ta rubuta a TikTok.

Yadda ta bankado sirrin

Da take ci gaba da kokawa, matashiyar ta ce ta gaza yin bacci tsawon kwanaki biyu da suke wuce kan lamarin. Kan yadda ta gano, matashiyar ta ce ta gani ne a shafin abokinsa.

Ta ce abokin ya wallafa hoton aurensa ne a shafinsa yayin da yake taya tsohon saurayin nata murna.

Kara karanta wannan

"Dan nan zai haddasa rigima": Bidiyon kyakkyawan yaro mai kama da mace ya tsuma zukatan jama'a

"...Na zata ni ce matar. Ban yi bacci ba tsawon kwanaki biyu da suka gabata kan haka saboda yana yi mani ciwo.
"...Ban san daga inda yarinyar ta fito ko yadda aka yi suka hadu ba. Ban sani ba," ta koka.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Mrs Jennifer Fred ta ce:

"Yar'uwata surayina da kansa ya turo mun katin gayyatar aurensa a WhatsApp..Na ce na tayaka murna...amma a yau na auri wanda na san yana sona kamar ya mutu."

Only 1 BubuStore in East ta ce:

"A kodayaushe ki dunga sanya saurayinki a shafi imma mai kyau ko mara kyau na sha fadin wannan, na saka hoton saurayina a wata shida da fara soyayyarmu kawata ta yi martani kan wallafata."

Jessica ta ce:

"Haka na saka saurayina na wata shida a shafina don taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa wata ta yi martani "ta yaya kika san saurayin goodness, baaba na shiga rudu."

Kara karanta wannan

"Himma ba ta ga rago": Dalibar Najeriya ta yi hijira zuwa turai, ta kama aikin noma gadan-gadan

Uwargida ta jinjinawa mijinta

A wani labarin kuma, wata yar Najeriya mai suna, Fatima Yusuf Nuhu, ta aika kalamai masu dadi ga mijinta yayin da ya auri tsohuwar dalibarta a matsayin mata ta biyu.

A ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, matar ta saki katin gayyatar auren mijinta, tana mai gayyatar mutane da su zo daurin auren a ranar 2 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel