Jerin Jami'o'in Addinin Musulunci 5 Da Ya Kamata Ku a Sani a Najeriya Tare Da Bayanai

Jerin Jami'o'in Addinin Musulunci 5 Da Ya Kamata Ku a Sani a Najeriya Tare Da Bayanai

Akwai Jami'o'in Musulunci da dama da aka kafa a Najeriya da nufin samar da ingantaccen ilimi bisa tsarin addinin musulunci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jaridar The Nation ta tattaro cewa wadannan jami'o'in suna bai wa ɗalibai ingantaccen ilimi da koyarwar Musulunci.

Manufar kafa irin waɗannan jami'o'in ita ce samar da mahallin da dalibai za su iya koyan darussa iri-iri tare da samun zurfin fahimtar shari'a da dabi'un addinin Musulunci.

Jami'o'in musulunci a Najeriya.
Jerin Jami'o'in Musulunci Guda 5 a Najeriya da Ya Kamata Ku Sani Hoto
Asali: Twitter

Jami'o'in suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ilimin Najeriya kuma suna ba da dama ga masu son yin karatu ta hanyar da ta yi daidai da shari'ar Musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

Legit Hausa ta tattaro muku jami'o'in Musulunci 5 da muke da su a Najeriya, ga su kamar haka:

1. Jami'ar Fountain

Wannan Jami’a mallakin kungiyar Nasrul-Lahi-Il-Fatih Society (NASFAT) ce kuma ita ke kula da harkokin makarantar, tana zama ne a jihar Osun.

Gwamnatin Tarayya ta ba ta lasisin yin aiki a matsayin jami’a mai zaman kanta a ranar 17 ga Mayu, 2007, bisa ga shawarar Hukumar Jami’o’i ta Kasa (NUC).

2. Jami'ar Al-Qalam da ke jihar Katsina

Jami’ar Al-Qalam wadda a da ake kira da jami’ar Katsina, tana kan titin Dutsinma a cikin birnin jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma a Najeriya.

An kafa Al-Qalam a shekara ta 2005, kuma ita ce jami'ar Musulunci ta farko mai zaman kanta a Najeriya.

Jami'ar Al-Qalam, Katsina.
Jerin Jami'o'in Addinin Musulunci 5 da Ya Kamata Ku a Sani a Najeriya Tare da Bayanai Hoto: Al-Qalam University Katsina
Asali: Twitter

3. Jami'ar Crescent

Fitaccen masanin harkokin shari'a kuma tsohon alkalin kotun ƙasa-da-ƙasa ta Hague, Mai Shari'a Bola Ajibola, shi ne ya kafa jami'ar Crescent da ke Abeokuta a shekarar 2005.

Kara karanta wannan

Daga farko zuwa karshe: Jami'a na kashe naira biliyan 5 kan duk wani dalibin likitanci

Jami'ar tana daya daga cikin manyan jami'o'in Musulunci a Najeriya kuma an kafa ta a karkashin inuwar kungiyar Islamic Mission for Africa (IMA).

Jami'ar Crescent ta samu lasisi a 2005 bayan amincewar Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Jami'o'i ta Kasa (NUC).

4. Jami'ar Al-Hikmah

Gidauniyar Musulunci ta Abdur-Raheem Oladimeji (AROIF) ce ta kafa Jami'ar Al-Hikmah da ke Ilorin a Najeriya a shekara 2005.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba wa jami'ar lasisin yin aiki a matsayin jami'a mai zaman kanta a ranar 7 ga Janairu, 2005 (Lasisi mai lamba 010).

5. Jami'ar Summit

Jami’ar Summit, wacce kungiyar Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria (ADSN) ta kafa a Offa, tana bayar da ingantaccen ilimi ga daukacin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da addini, kabila, jinsi ko akida ba, amma bisa tsarin addinin Musulunci.

Jami’ar ta samu lasisin wucin gadi (Jami’a ta 59 mai zaman kanta) wanda NUC ta bata a ranar 5 ga Maris, 2015, kana ta samu Lasisin aiki na dindindin a ranar 1 ga Afrilu, 2019.

Kara karanta wannan

Rikicin kungiyar Izala ya yi sanadiyyar tafiya kotu, an rufe masallaci na shekaru 7

Jerin Sunayen Manyan Jami'o'i 20 Mafi Kyau a Duniya

A wani rahoton kuma QS World University Rankings ya wallafa jerin fitattun jami'o'i na sahun gaba a muhallin karatu na shekarar 2024 mai zuwa.

Makarantar fasaha ta Massachusetts, jami'ar Cambridge da jami'ar Oxford ne suka mamaye matsayi ukun farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel