Daga Farko Zuwa Karshe: Jami’a Na Kashe Naira Biliyan 5 Kan Duk Wani Dalibin Likitanci

Daga Farko Zuwa Karshe: Jami’a Na Kashe Naira Biliyan 5 Kan Duk Wani Dalibin Likitanci

  • Jami'o'in Najeriya sun koka kan karancin kudin da suke samu don gudanar da ayyukan horas da dalibai, musamman na fannin likitanci a kasar
  • Kwamitin shugabannin jami'o'i CVCNU ya yi wannan korafin, inda ya yi nuni da cewa kowanne dalibin likitanci na lakume naira biliyan biyar
  • Kwamitin ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati kadai ba za ta iya daukar nauyin ilimantar da dalibai ba, dole daliban su ma su tashi tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kwamitin shugabannin jami'o'in Najeriya ya koka kan karancin kudin da jami'o'i ke samu daga gwamnati wanda ke jawo koma baya ga harkar koyarwa a jami'o'in gwamnati.

Ya bayyana cewa jami'o'i na kashe naira biliyan 5 wajen horas da kowanne dalibin likitanci guda daya, walau makarantar gwamnati ko ta kudi, don haka akwai bukatar fara raba dai dai.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Gwamnonin Arewa sun hadu a Kaduna, karin bayani kan abin da za su tattauna

Jami'o'i na kashe Naira biliyan 5 wajen horas da kowanne dalibin likitanci guda daya
Farfesa Ochefu ya ce jami'o'i na kashe Naira biliyan 5 wajen horas da kowanne dalibin likitanci guda daya. Hoto: Jamb Prime, CVCNigeria (A kula: An yi amfani da hoton daliban don buga misali kawai)
Asali: Facebook

Akwai gibi a biyan kudin da jami'o'i ke amfani da su - CVCNU

Babban sakataren kungiyar CVCNU, Prof Yakubu Ochefu, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Alhamis a wani taron horaswa da na manyan jami'an tsaffin daliban jami'o'i.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kwamitin ne ya zauna ya binciko kudin da ake kashewa wajen ilimantar da daliban a jami'o'in gwamnati da na kudi, rahoton Daily Trust.

Premimun Times ta ruwaito Ochefu na cewa akwai babban gibi da ake samu daga bangaren gwamnati da dalibai na biyan kudin da jami'o'in ke kashewa wajen bayar da ilimi.

Gwamnati kadai ba za ta iya daukar nauyin ilimin dalibai ba - Prof Ochefu

Shugaban kungiyar ya ce:

"Idan da ace gwamnati za ta dauki nauyin horas da daliban, to za ta rinka biyan Naira biliyan biyar ga jami'o'i don horas da kowanne dalibi daya.

Kara karanta wannan

Wike Vs Fubara: Karin kwamishinoni biyu sun yi murabus a jihar Rivers, adadin ya kai 6 yanzu

"Don haka iya kudinka ne iya shagalinka, ba za ka ba shugaban jami'a naira miliyan uku ya horas da dalibin da ke cin Naira biliyan biyar ba, kuma kowa ya ga abin da ke faruwa yanzu."

Duk da hakan, Ochefu ya ce gwmanati kadai ba za ta iya daukar nauyin ilimantar da dalibai ba.

Kotu ta ba da umurnin rataye matashin da ya cinnawa mahaifiyarsa wuta a Niger

A wani labarin kuma, wata babbar kotu mai zama a jihar Niger, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rayata ga wani Stephen Jiya wanda ta same shi da laifin kashe mahaifiyarsa.

A cikin watan Disamba 2021 ne Jiya ya babbake mahaifiyarsa mai shekaru 61 kan zarginta da zama silar bacewar matarsa a garin Suleja, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel