Jerin Sunayen Manyan Jami'o'i 20 Mafi Kyau a Duniya Na Shekara Mai Zuwa 2024

Jerin Sunayen Manyan Jami'o'i 20 Mafi Kyau a Duniya Na Shekara Mai Zuwa 2024

  • QS World University Rankings ya wallafa jerin fitattun jami'o'i na sahun gaba a muhallin karatu na shekarar 2024 mai zuwa
  • Makarantar fasaha ta Massachusetts, jami'ar Cambridge da jami'ar Oxford ne suka mamaye matsayi ukun farko
  • Jerin ya ƙunshi makarantu 1,500 daga sassa daban-daban 104 na duniya kuma ya maida hankali ne kan aiki da ɗorewa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

London, UK - Cibiyar Fasaha ta Massachusetts (MIT) ta zama ta ɗaya a jerin manyan makarantun neman ilimi na duniya da aka fitar na shekarar 2024 mai zuwa.

Jerin manyan jami'o'in duniya 20.
Jerin Fitattun Jami'an Duniya da Aka Fitar na Shekarar 2024 Mai Zuwa Hoto: Jim Stephenson/View Pictures/Universal Image Group
Asali: Getty Images

Hakan na ƙunshe ne kunshin jerin manyan jami'o'in duniya wanda 'QS World University Rankings' ya fitar karo na 20 wanda ya kunshi makarantu 1,500 daga wurare 104.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 8 da suka bada taimakon miliyan 700 da aka kashe masu Maulidi a Tudun Biri a Kaduna

Jami'o'in ƙasar Burtaniya guda biyu, Cambridge da Oxford, sune suka zo na biyu da na uku bi-da-bi, wanda ya sa suka zama jami'o'i uku mafi kyau a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

QS World University Rankings, sune kaɗai suka saba fidda jerin manyan makarantu mafi kyau da babu nau'insa a duniya ta hanyar duba ɗaukar aiki da ɗorewa.

Jerin manyan jami'o'i 20 mafi kyau a duniya

1. Cibiyar Fasaha ta Massachusetts (MIT)

2. Jami'ar Cambridge

3. Jami'ar Oxford

4. Jami'ar Havard

5. Jami'ar Stanford

6. Kwalejin Imperial da ke birnin Landan

7. ETH Zurich

8. Jami'ar Singapore ta ƙasa

9. University College ta Landan

10. Jami'ar California

11. Jami'ar Chicago

12. Jami'ar Pennsylvania

13. Jami'ar Cornell

14. Jami'ar Melbourne

15. Makarantar fasaha ta California

16. Jami'ar Yale

17. Jami'ar Peking

18. Jami'ar Princeton

19. Jami'ar kudancin Wales

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, 'yar majalisa ta yi amai ta lashe, ta sauya sheƙa daga APC zuwa PDP

20. Jami'ar Sydney

ECOWAS ta amince zata cire wa Nijar takunkumi bisa sharaɗi

A wani rahoton na daban Shugaban majalisar kungiyar ECOWAS , Sidie Tunis ya ce za a janye takunkumin da aka kakabawa Nijar amma da sharadi.

Sidie Tunis ya yi wannan bayani ne a lokacin da tawagar ‘Africans Without Borders’ ta kai masa ziyara a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel