Shugaban Sojojin Najeriya Ya Ziyarci Kaduna Bayan Mummunan Harin Bam da Ya Kashe Masu Maulidi 85

Shugaban Sojojin Najeriya Ya Ziyarci Kaduna Bayan Mummunan Harin Bam da Ya Kashe Masu Maulidi 85

  • Hafsan rundunar soji Laftanal Janar Lagbaja ya yi takanas zuwa Kaduna inda jirgin yakin soji ya saki bam kan fararen hula
  • A ranar Lahadi ne wani jirgin yakin soji ya saki bam kan wasu masu maulidi a garin Tudun Biri, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna
  • Hafsan sojin ya ziyarci jihar Kaduna domin gani da idonsa irin barnar da harin ta yi a garin, wanda aka rasa rayukan akalla mutum 85

Jihar Kaduna - Hafsan sojin kasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja, ya ziyarci jihar Kaduna kwana biyu bayan harin sojin ta sama da ya halaka sama da mutum 85 yayin da ya jikkata Wasu da dama.

Hafsan sojan ya kai ziyarar ne don gani da idonsa irin barnar da aka yi wa al'ummar garin, tare da jajanta wa wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Maulidi: Atiku ya yi martani kan harin bam da aka yi kan bayin Allah a Kaduna, ya ba da shawara

Taoreed Lagbaja/Kaduna
Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya kai ziyarar ne don gani da ido kan irin barnar da harin ya yi a garin. Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Waki'ar ranar Lahadi na daga cikin manyan hare-haren da dakarun soji suka kaddamar bisa kuskure, Channels TV ta ruwaito.

Kuskure ne harin da aka kai kan masu maulidi, rahoto

Tun da farko dai, rundunar sojin ta amsa laifin cewa daya daga cikin jiragen yakin ta ne ya saki bama-baman wanda ya rutsa da masu maulidi a garin Tudun Biri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da rundunar ba ta bayar da kiyascin wadanda abin ya rutsa da su ba, sai dai mazauna garin sun ce aƙalla mutum tamanin da biyar, ciki har da mata da kananan yara ne suka mutu a harin.

Rahotannin rundunar ya nuna cewa jirgin na gudanar da wani sintiri ne lokacin da tsautsayi ya sa ya saki bam a garin.

A yayin ziyarar, shugaban sojin ya roki afuwar iyalan da abin ya shafa, tare da shan alwashin dakile hakan daga sake faruwa, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A Dangi 1 kadai, Sojoji sun kashe mutane 34 da bama bamai wajen Maulidin Kaduna

Tinubu da Uba Sani sun dauki mataki

Tuni dai shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani suka bayar da umurnin yin binciken gaggawa kan lamarin.

Tinubu ya kuma bayar da umurnin bai wa wadanda suka tsira daga harin duk wata kulawa da suke bukata a asibiti tare da yin addu'ar gafara ga wadanda suka mutu a harin.

Hukumomin tsaron Najeriya musamman na soji, na fifita hare-haren sama da sunan yaki da 'yan ta'adda a yankunan Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas.

COP28: Gwamnatin Tinubu ta fadi adadin wakilan da ta tura Dubai

A wani labarin na daban, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce wakilai 442 ne kawai ta dauki nauyin su zuwa taron dumamar yanayi da ke gudana a Dubai, Legit Hausa ta ruwaito.

Jerin jadawalin sunayen ya nuna cewa an tura wakilai 32 daga hukumar dumamar yanayi ta kasa, sai ma'aikatar muhalli mutum 34, da wasu ministoci

Asali: Legit.ng

Online view pixel