Boko Haram: Kungiyar Tarayyar Turai, EU Za Ta Tallafawa Arewa Maso Gabas

Boko Haram: Kungiyar Tarayyar Turai, EU Za Ta Tallafawa Arewa Maso Gabas

  • Tawagar kungiyar tarayyar Turai ta kai ziyara zuwa jihar Borno domin duba yadda lamuran tsaro ke guda a yankin Arewa maso gabas
  • Jakadan kasar Netherlands, Wouter Plomp ne ya jagoranci tawagar zuwa Maimalari da ke jihar Borno a jiya Laraba, 15 ga watan Mayu
  • Rundunar sojin Najeriya karkashin jagorancin Manjo Janar Waidi Shaibu ne ta karbi tawagar tare da bayyana musu halin da ake ciki a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Tawagar kungiyar tarayyar kasashen turai (EU) ta gana da sojojin Najeriya da ke taki da ƴan ta'adda a jihar Borno.

EU ARMY
Kungiyar tarayyar turai ta ziyarci jihar Borno kan yaki da ta'addanci. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

A jiya Laraba, 15 ga watan Mayu ne tawagar ta isa jihar Borno tare da wakilan kasar Netherlands.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kama rijiyoyin mai na bogi a jihar Ribas

Jakadan kasar Netherlands, Wouter Plomp ne ya jagoranci tawagar zuwa Maimalari da ke Maiduguri domin ganawa da sojojin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zuwan tawagar EU Borno

Jawabin da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafin ta na Facebook ya nuna cewa tawagar ta je Borno ne domin duba yadda lamura ke gudana a jihar.

Sun je ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki ciki har da sojojin Najeriya kan duba yadda za a farfaɗo da yankunan da ayyukan ta'addanci suka yiwa illa.

Yayin da yake jawabi, jakadan kasar Netherlands ya ce lalle za su cigaba da kokari wurin bada gudunmawa kan yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso gabas.

Jawabin jami'an sojin Najeriya

Kwamandan rundunar operation haɗin kai (OPHK), Manjo Janar Waidi Shuaibu ya yaba wa tawagar bisa kokarin da suke kan taimakon yankin.

Kara karanta wannan

Katsina: "Yadda 'Yan Bindiga Suka Shirya Tuggu, Suka Kashe Sojoji" Inji DHQ

Haka zalika Kyaftin MA Abdullahi ya bayyana wa tawagar irin halin da ake ciki na yaki da ƴan ta'adda a yankin.

EU ta saka takunkumi ga Iran

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar tarayyar turai (EU) ta sanar da sabon takunkumi da ta kakabawa Iran a matsayin horo kan harin da ta kai a Isra'ila.

Shugabannin kungiyar sun dauki matakin ne bayan wani taron gaggawa da suka yi a birnin Brussels bayan fara rikicin Iran da Isra'ila.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel