“Kada Ka Biya Sadaki”: Budurwa Ta Fashe da Kuka Yayin da Ta Roki Dan Aikin Davido Ya Aureta a Bidiyo

“Kada Ka Biya Sadaki”: Budurwa Ta Fashe da Kuka Yayin da Ta Roki Dan Aikin Davido Ya Aureta a Bidiyo

  • Israel DWM, hadimin shahararren mawakin Najeriya Davido, ya zama bazawari mai zafi a gari
  • A kwanan nan ne wata budurwa mai suna Ella Ada, ta yi fice a soshiyal midiya kan ta roki Isreal ya aureta
  • A cewar Ella, tana son hadimin Davido din sosai kuma tana so ta taimaka masa domin ya manta da tunanin aurensa da ya mutu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Hadimin shahararren mawakin Najeriya Davido, Isreal Afaere wanda aka fi sani da Isreal DMW, ya hau kanen labarai saboda mutuwar aurensa.

Wata matashiyar budurwa, Ella Ada, ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin fallasa sirrin zuciyarta na irin son da take yi wa Isreal yayin da ta roke shi da ya taimaka ya aureta.

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

Cikin kuka budurwa ta roki Isreal da ya aureta
“Kada ka biya sadaki”: Budurwa ta fashe da kuka yayin da ta roki dan aikin Davido ya aureta a bidiyo Hoto: @isrealdmw
Asali: Instagram

A cikin bidiyon, an gano Ella tana sharban kuka wiwi yayin da take bayyana dalilan da yasa take so Isreal ya aureta da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ella, bata so Isreal ya kasance cikin damuwa kuma kan mutuwar aurensa. Bata tsaya a nan ba, ta kara da cewar tana son matashin sosai yayin da take rokon Allah ya amsa addu'arta na son ganinsu tare.

Domin ta nuna da gaske take, matashiyar ta bayyana cewa kada Isreal ya damu da biyan sadakinta saboda ita ba kudinsa take so ba kuma ta san cewa ya kashe kudi sosai a aurensa da ya mutu.

Ella ta rubuta a jikin bidiyon:

"Idan na kalli cikin idanunka, ina iya ganin yadda rayuwarmu zata kasance a tare.mafarkina shine mu kasance sannan mu bunkasa a tare, idan na ganka,zuciyata na duka da sauri da sauri, ba wai don tsoro ba sai da so da nake maka ISREAL. Ka ceceni daga nutsewa,ina fadawa cikin kogin kauna; na zauce cikin sonka ISREAL DMW. Sun ce so makaho ne,ka rigada ka makanta ni.zan ci gaba da sonka har abada."

Kara karanta wannan

Amarya ta fasa aurenta yayin da angon ya gindaya mata sharudda 4 gabannin aurensu

Kalli bidiyonta a kasa:

Martani yayin da budurwa ta koka da rokon Isreal DMW kan ya aureta

Bidiyon matashiyar da ta furta so da muradin auren Idreal DMW ya haddasa cece-kuce a tsakanin al'umma.

showy_sleem:

"Hauka ko zazzabin cizon sauro."

Rita_nazy:

"dariya zai kashe ni a nan."

jay_osas:

"Ba zai yi shagalin biki ba kuma saboda Davido ba zai zo ba don na san Davido kuke son gani lol."

its.kemzy_':

"Wani ya fara nunawa mahaifiyarta bidiyon nan tukuna."

Iam_wildrex:

"Wannan shi muke kira hauka tsantsa."

Auren diyar Abacha da Buni ya mutu

A wani labari na daban, mun ji cewa aure ya mutu tsakanin gwamnan Yobe, Mai Mala Buni da Gumsu Sani Abacha.

Diyar marigayi shugaban mulkin soja Sani Abacha ta bayyana rabuwar auren ta yayin da take mayar da martani ga wani mai sharhi da ya kira ta da “uwargidan gwamna” a kan shafinta na X @G_sparking a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel