Wani ɗalibin kwalejin fasaha ya mutu yana tsaka da saduwa da budurwarsa a Hotel

Wani ɗalibin kwalejin fasaha ya mutu yana tsaka da saduwa da budurwarsa a Hotel

  • Wani ɗalibi da ya gama Diploma a matsayin mafi hazaƙa, Daniel, ya mutu ya na tsaka da holewa da budurwarsa a Otal
  • Hukumar makarantar Ibadan Poly inda ya ke karatun babban Diploma ta ce lamarin babu daɗi, zata cigaba da shawartar dalibai
  • Lamarin ya faru ne bayan ɗalibin ya dawo makaranta da nufin fara jarabawa amma aka ɗage zuwa wani lokaci

Ibadan, jihar Oyo - Wani ɗalibi da ke karatun babbar Diploma (HND 1) a kwalejin Fasaha ta Ibadan (Ibadan Poly), Igunu Oromidayo Daniel, ya mutu yana cikin saduwa da budurwarsa.

Daily Trust ta rahoto cewa budurwar mai suna, Aramide, ita ma ɗaliba ce da ke karatun Diploma aji biyu (ND 2) a kwalejin, lamarin ya faru ne a Apete, ƙaramar hukumar Ido, jihar Oyo, ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Wata Budurwa ta maka mahaifinta gaban Kotun Musulunci a Kaduna kan Soyayya

Ɗaliban biyu, waɗan da suka je makaranta da nufin fara jarabawar zangon karatu na farko, sun koma gida a Oyo bayan hukumar makarantar ta ɗage ranar fara jarabawan.

Daliban Ibadan Poly biyu.
Wani ɗalibin kwalejin fasaha ya mutu ya tsaka da saduwa da budurwarsa a Hotel Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa da tsiya aka raba Ɗalibin da budurwarsa wacce ya mutu ya bari rai hannun Allah, yanzu haka tana kwance a Asibitin koyarwa na Ibadan (UCH Ibadan).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu ɗalibai yan uwansa sun bayyana cewa an gano gawarsa ne a Hotel ɗin da saurayin ya kama dukkan su tsirara, budurwar na kan Daniel.

Wani ɗalibi da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce Daniel ya mutu ne sanadiyar tsanananin jima'i yayin da ya bar masoyiyarsa rai hannun Allah.

Hukumar makaranta ta tabbatar da lamarin

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun Poly Ibadan, Alhaji Adewole Soladoye, ya bayyana abin da ya faru da rashin sa'a kuma abin takaici.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ministan albarkatun man fetur ya janye daga takarar shugaban kasa a 2023

Punch ta rahoto Ya ce:

"Eh dagaske ne kuma abun takaici ne, muna jajantawa iyalansa. Daniel ne ɗalibi ma fi kwazo da ya kammala diploma a lokacinsa, makon da ya gabata ɗan uwansa ya rasu kuma ya je jana'izarsa ranar Lahadi."
"Ya dawo makaranta saboda fara jarabawa kuma ya mutu ranar Litinin. Ba zamu iya cewa ga abinda ya yi sanadin mutuwarsa ba, ita kuma macen da suke tare muna mata fatan samun lafiya."
"Mun samu labarin likitoci na kokarin ceto rayuwarta. Kwaleji ba ta ji dadin abin da ya faru ba kuma a matsayin iyaye zamu cigaba da ba ɗalibai shawari, muna son mahaifa su taka rawar su."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun bayyana sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

Miyagun yan bindiga sun aike da wasika ɗauke da jerin sunayen wasu kananan hukumomi 9 da zasu kai hari nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi, yace sun gama wahala a duniya

Hakan ya zo ne awanni bayan wasu mahara sun farmaki karamar hukuma da Kotu, inda suka aikata ɓarna mai yawa duk a Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel