An Tsinci Gawar Wata Budurwa a Otel Bayan Ta Bi Wasu Maza Da Suka Yi Alƙawarin Biyanta N50,000 Ta Kwana Da Su

An Tsinci Gawar Wata Budurwa a Otel Bayan Ta Bi Wasu Maza Da Suka Yi Alƙawarin Biyanta N50,000 Ta Kwana Da Su

  • An gano gawar wata budurwa mai suna Ugochi Nworie a wani otel inda rahotanni suka ce an cire wasu sassan jikinta
  • Kawayenta sun bayyana cewa ta bi wasu maza ne zuwa otel su kwana bayan sun mata alkawarin za su biya ta N50,000
  • Daya cikin kawayen Ugochi ta ce ita ma an mata tayin kwana da wani kan N100,000 amma ta ki domin ba ta san su ba

Ebonyi - An kashe wata yarinya mai shekaru 20 da yan kai, Ugochi Nworie a daren ranar Asabar a wani fitaccen otel (da aka sakayya sunansa) a kan babban hanyar Enugu zuwa Abakaliki, Vanguard ta rahoto.

Yayin da wani rahoto ya nuna an ci zarafinta, wani rahoton daban ya ce masu kashe al'umma don yin asirin neman kudi ne suka kashe ta a Ebonyi.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Yarinyar, wacce aka ce yar asalin karamar hukumar Ikwo, a Jihar Ebonyi ne, ta hadu da wasu maza ne a otel, bayan casu da aka yi cikin dare.

An Yi Wa Mata Budurwa Kisar Gilla a Ebonyi Bayan Ta Bi Wasu Maza Otel Saboda N50,000
An tsinci gawar wata budurwa a otel bayan ta bi wasu maza da suka yi alkawarin biyanta N50,000 ta kwana da su. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Vanguard ta tattaro cewa mazan sun taho da wata mota wacce aka rubuta 'Colonel' a jikinta, kuma suka yi yarjejeniya cewa za a biya budurwar N50,000 domin ta kwana da daya daga cikinsu, kuma ta amince da hakan.

Rahotanni sun ce an gano gawar budurwar a otel din a ranar Lahadi da rana bayan kawayenta sun kai korafi kan bacewarta a ofishin yan sanda.

Wasu majiyoyi na kusa da marigayiyar sun ce an cire wasu sassan jikinta masu muhimmanci sannan an kai gawarta dakin ajiye gawa a Abakaliki.

Wata majiyar ta ce an gano gawar ta ne a ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022, kwana daya bayan sun isa otel din a mahadar G-Hostel, Abakaliki, babban birnin jihar tare da wasu maza.

Kara karanta wannan

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

Yan sanda sun tabbatar da rasuwar Ugochi

Kakakin yan sandan jihar, a ranar Laraba a Abakalilki, Loveth Odah, ta ce ana bincike don gano wadanda suka kashebudurwar don a hukunta su.

Mun gargade ta kada ta bi su amma ta ki yarda

Daya daga cikin kawayen Ugochi wacce ta nemi a boye sunanta ta ce:

"Bayan mun gama casu a otel din da Ugochi, za mu tafi gida amma Ugochi ta tsaya tare da wasu maza soboda sun ce za su biya ta N50,000 ta kwana da dayansu.
"Sun ce za su bani N100,000 amma ban yarda ba saboda ban san su ba. Na yi musu karya cewa saurayi na yana gari don haka, za zan iya kwana a waje ba.
"Mun gargadi Ugochi amma ta bi su saboda kudin. Mun kyalle ta mun tafi gida. Da bamu ganta da safe ba sai muka tafi muka yi korafi wurin yan sanda.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun sheke na kusa da Shekau bayan yunkurin mika kansa ga sojoji

"Mun ji mazan suna fada wa wasu cewa daga Ghana suke. Ba mu san ko gaskiya bane. Mun ga an rubuta "Colonel" a jikin motan daya daga cikinsu wurin lamba.
"Ugochi ce ta kashe kanta. Idan da ta saurare mu, da ba ta mutu ba. Abin ciwo da takaici ne."

An Tsinci Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya a Ɗakin Otel Sati Ɗaya Bayan Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarta

A wani rahoton, an tsinci gawar Jaruma Takor Veronica a cikin wani daki na Otel a Jihar Benue, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A cewar rahotanni daban-daban, an gano gawar na Veronica ne kimanin sati baya bayan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta.

An rahoto cewa an tsinci gawarta ne a wani dakin otel a unguwar Nyinma na Makurdi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel