Ma’aikatan Tarayya 2,000 Sun Rasa Albashin Watan Nuwamba, An Gano Dalilin Hakan

Ma’aikatan Tarayya 2,000 Sun Rasa Albashin Watan Nuwamba, An Gano Dalilin Hakan

  • Rahotanni sun bayyana cewa akalla ma'aikatan gwamnatin tarayya dubu biyu ne ba za su samu albashin watan Nuwamba ba
  • Hakan ya biyo bayan wata tantancewa da ofishin shugaban ma'aikatan tarayya da kuma samun matsala a tsarin IPPIS
  • A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne gwamnatin tarayyar ta fara biyan ma'aikatanta albashi, inda wasu ba za su ga na su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Akalla ma'aikatan gwamnatin tarayya dubu biyu ne suka rasa albashin su na watan Nuwamba, kamar yadda majiya mai tushe ta bayyana hakan a ranar Litinin.

Wani ma'aikaci gwamnati a ma'aikatar tsaro ta kasa, ya yi nuni da cewa da yawa daga cikin ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatar ba su samu albashin su ba.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir ya sanya yan fansho kuka yayin da ya cika musu alkwarin da ya dauka, ya koka

Ma'aikata 2,000 ba za su samu albashin Nuwamba ba.
Akalla ma'aikata dubu biyu ne ba su samu albashin su ba sakamakon gaza tantacewar tsarin IPPIS. Hoto: TUCNigeria/ASCSN
Asali: UGC

Ma'aikacin gwamnatin ya kuma yi nuni da cewa gaza samun albashin ba zai rasa nasaba da tantancewa da ofishin shugaban ma'aikatan tarayya da ke yi a kasar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa ma'aikata ba za su samu albashin watan Nuwamba ba?

Legit ta ruwaito wani ma'aikaci a wata babbar ma'aikatar tarayya ya bayyanawa cewa wani kaso na ma'aikata ba su samu albashin su ba saboda matsalar IPPIS.

Ya ce:

"Akalla ma'aikata dubu biyu ne ba su samu albashin su ba sakamakon gaza tantacewar tsarin IPPIS."

Ko da aka tuntube shi, mai magana da yawun ofishin babban akawu na kasa, Bawa Mokwa, ya ce:

"A ranar Alhamis aka fara sakin albashi. Ba duka ma'aikata ne za su samu ba. Idan na samu karin bayani daga datakan IPPIS, zan dawo gare ka."

Shugaban kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati, Tommy Etim, ya shaidawa wakilin jaridar cewa ofishin shugaban ma'aikatan tarayya ya fara aiki kan lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba na Kano zai faranta ran tsofaffin ma’aikata, an tsaida ranar fara biyan kudin giratuti

Da gaske gwamnati ta yi gwanjon babban otel mallakin jihar Kwara?

A wani labarin na daban, a yayin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa an cefanar da babban otel mallakin jihar Kwara, gwamnatin jihar ta fito ta yi martani akai.

Gwamnatin jihar ta ce babu wani dalili da zai saka a sayar da otel din, kawai ta yi gwanjon kayan cikinsa ne don yin gyare-gyare, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel