Da Gaske Gwamnati Ta Yi Gwanjon Babban Otel Mallakin Jihar Kwara? Gaskiya Ta Bayyana

Da Gaske Gwamnati Ta Yi Gwanjon Babban Otel Mallakin Jihar Kwara? Gaskiya Ta Bayyana

  • A yayin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa an cefanar da babban otel mallakin jihar Kwara, gwamnatin jihar ta fito ta yi martani akai
  • Ba tun yanzu ne ake samun takun saka tsakanin abokan hamayya da gwamnati kan otel din ba, sai dai na wannan karon ya fi zafi
  • Gwamnatin jihar ta ce babu wani dalili da zai saka a sayar da otel din, kawai ta yi gwanjon kayan cikinsa ne don yin gyare-gyare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta karyata jita-jitar da ake yadawa na cewar ta sayar da babban otel din jihar Kwara, a lokacin da ta ke sayar da kayayyakin ciki.

Kara karanta wannan

Dirama yayin da dan takarar gwamnan PDP ya gagara magana da yarensu, ya nemo mai fassara

Otel din ya dade yana jawo cece-ku-ce tsakanin abokan hamayya da gwamnatin jihar.

Kwara Hotel
Gwamnatin jihar Kwara ta ce babu wani dalili da zai aka ta sayar da otel din. Hoto: Hotels.ng
Asali: UGC

Kayayyakin da aka yi gwanjonsu a otel din

An gudanar da gwanjon kayayyakin ne a karshen makon da ya gabata, inda aka ga ana sayar da firinji akan naira dubu ashirin, manyan gadaje da katifu akan Naira 40,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran kayayyakin da aka siyar sun hada da fankoki, na'urar sanyaya daki, abin shimfidawa a kasa, da wasu kayayyakin, Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanoni takwas ne suka nemi yin takara wajen sayen kayayyaki, amma aka zabi guda hudu.

Ba za a sayar da otel din ba komai rintsi - Gwamnati

A watan Oktoba na shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kwara ta rufe otel din domin yin gyare-gyare da yin garambawul na gudanarwarsa.

Da ya ke martani kan zarge-zargen da ake yi, kwamishinan kasuwanci, kirkira da fasaha na jihar, Hon Damilola Yusuf, ya ce:

Kara karanta wannan

Bani da katabus: Wanda ya kone takardar digirinsa ya yi bayanin dalilansa na bankawa takardunsa wuta

"Otel din kayan gwamnati ne kuma abin alfahari ne a jihar wanda ba za a iya sayar da shi akan kowanne dalili ba."

Majalisar jihar Kwara ta yi sabon shugaban masu rinjaye

A wani labarin na daban, majalisar jihar Nasarawa ta nada sabon shugaban masu rinjaye da mataimakinsa, da kuma mataimakin bulalar majalisar.

Sabon kakakin malisar jihar Nasarawa, Danladi Jatau ya sanar da nadin manyan mukaman guda uku a zauren majalisar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel