Tsarin IPPIS baƙon abu ne da ba zai karbu ba a Najeriya - ASUU

Tsarin IPPIS baƙon abu ne da ba zai karbu ba a Najeriya - ASUU

Kungiyar malaman jami’o’in a Najeriya ASUU, ta bayyana sabon tsarin biyan albashi na IPPIS wanda gwamnatin tarayya ta kawo a matsayin bakon abu da ta aro daga ketare.

ASUU yayin bayyana takaici kan tsarin na IPPIS, ta ce "ko kadan kayan aro ba ya ado kuma ba zai taba rufe katara ba."

Shugaban kungiyar reshen Jami’ar Fatakwal, Dakta Austen Sado, ya bayyana mamaki kan yadda dukkan bayanan ma’aikatan gwamnatin Najeriya kacokan su ke a hannun wata kasar ta daban.

Shugaban ASUU na Najeriya; Farfesa Biodun Ogunyemi
Shugaban ASUU na Najeriya; Farfesa Biodun Ogunyemi
Asali: UGC

Da ya ke ganawa da manema labarai na jaridar The Punch, Dr. Sado ya yi bayanin cewa, gwamnatin tarayya ta yi riko da abun aro watau tsarin biyan albashin ma’aikata na IPPIS.

Ya ce a madadin haka, gwara gwamnatin ta karbi tsarin biyan albashin na gaskiya da hakika da jami’o’in kasar ke amfani da shi wanda a nan cikin gida aka kirkiro ba daga wani wurin ba.

Ya zayyana cewa, kungiyar tana ci gaba da kirdado da jiran tsammanin amsa goron gayyatar gwamnatin tarayya domin yi mata bayani dalla-dalla dangane da tsarin na biyan albashin da jami’o’in kasar suka kirkiro.

KARANTA KUMA: Haraji: A kowane mako, mu na tatsar N3bn a dalilin kudin hatimi – Nami

Sai dai ya bayyana takaici dangane da yadda gwamnatin ba ta nuna ra’ayi ko kadan a kan hakan ba, a yayin da ta ke ci gaba da ikirarin ita gwamnati ce mai yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaban kungiyar ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta sake yin dogon nazari a kan tsarin na IPPIS musamman a wannan zamani da ake fama da masu kutsen sace bayanai da damfara ta yanar gizo.

Legit.ng ta ruwaito cewa, alamu masu karfi sun bayyana a karshe mako cewa gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, za su koma kan teburin sulhu domin kawo karshen yajin aikin malamai suka shafe watanni hudu suna yi.

Binciken manema labarai na jaridar This Day ya gano cewa, nan ba da dadewa ba, bangarorin biyu za su fara tattaunawa domin sulhunta sabanin da ke tsakaninsu.

Bangarorin biyu za su koma kan teburin sulhu domin sabunta tattaunawa kan rashin jituwar da ke tsakaninsu musamman a kan sabon tsarin biyan albashi na bai daya da gwamnatin ta dage a kan sanya malaman jami’o’i cikinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel