Ana Ta Kukan Tarin Bashi, Gwamnatin Tinubu Za Ta Runtumo Rancen $2.25Bn Daga Bankin Duniya

Ana Ta Kukan Tarin Bashi, Gwamnatin Tinubu Za Ta Runtumo Rancen $2.25Bn Daga Bankin Duniya

  • Rahotanni sun ce Najeriya na sa ran karban bashin $2.25bn daga Bankin Duniya a watan Yunin 2024 domin bunkasa harkokin tattalin arziki
  • Za a raba bashin da za a karbo ne a wasu muhimman ayyuka guda biyu don inganta rashin samun kudaden shiga da kuma tabbatar da makomar tattalin arzikin kasar
  • Sabon bashin zai daga yawan bashin Najeriya zuwa kusan $45bn, inda rahoto ya bayyana kasashe biyar mafi yawan tara bashi

Akwai yiwuwar Bankin Duniya ya amince da ba Najeriya rancen $2.25bn a ranar 13 ga Yuni, 2024 don yin wasu muhimman ayyuka guda biyu.

Wasu takardu daga hukumonin Najeriya sun nuna cewam za a raba kudaden da za a karbo ne tsakanin ayyukan don bunkasa tattalin arzikin Najeriya da karfafa tattara albarkatun kasa.

Tinubu zai ci bashin da zai kai $2.25bn
Za a kara ci wa Najeriya bashin $2.25bn nan kusa | Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Wasu ayyuka da za a yi da kudin?

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

Daya daga cikin ayyukan da aka yiwa lakabi da REST zai mai da hankali ne ga yadda za a farfado da tattalin arzikin Najeriya da kawo sauye-sauye wajen samar da kudaden shiga, inda aka ce zai ci $1.5bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma na biyun; ARMOR da zai maida hankali ga rarraba albarkatu da amfani dasu yadda ya dace da aka tsara zai ci akalla $750m.

Rahotanni sun ce ana ci gaba da tattaunawa tsakanin masu ba da rancen da gwamnatin Najeriya domin kammala sharuddan da aka tsara.

Tattaunawar na da mahimmanci sosai saboda ita za ta ba shirin armashi da kuma taswirar yadda za a tafiyar dashi.

Sakamakon da ake tsammani daga cin bashin

Ana sa ran kudaden za su bunkasa kokarin Najeriya na sake fasalin manufofin tattalin arziki da inganta ayyukan gwamnati, wanda ke da matukar muhimmanci ga dorewar kudi da tattalin arzikin kasar na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin janye harajin shigo da kaya, ana sa ran saukar farashin abinci

Shirin ARMOR zai ba da karfi ne wajen inganta kudaden shiga ba ta fannin man fetur ba daga 2024 zuwa 2028 a matakin tarayya, tare da mai da hankali kan haraji da garambawul a ma’aikatu.

Wasu bayanai daga Ofishin Kula da Bashi (DMO) a baya-bayan nan sun nuna inda ake bin Najeriya tarin bashi.

Irin bashin waje da ake bin Najeriya

Bayanai daga DMO sun nuna cewa bashin Najeriya na waje ya kai $42.469bn a watan Disamba na 2023.

Binciken manyan masu bin Najeriya sun hada da Bankin Duniya, IMF AfDB da dai sauransu, kamar yadda rahoto ya bayyana.

Babban Bankin Duniya na bin Najeriya $15bn, bankin Exim na kasar China na bin Najeriya $5.167bn, IMF $2.469bn, sai kuma bashin $1,652bn daga bankin raya Afirka (AfDB).

Yadda ake bin bashin Najeriya makudan kudade

A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa ana bin Najeriya bashin fiye da Naira tiriliyan 87 a karshen watan Yuni na 2023.

Kara karanta wannan

InnaliLahi: Mutane 30 sun mutu a wani mummunan ibtila'i da ya rutsa a Arewa

Bashin kamar yadda Hukumar Gudanar da Bashi (DMO) ta tabbatar ya karu zuwa tiriliyan 87 ne daga 49.89 a watan Disambar 2021.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta tabbatar da shi a yanar gizonta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel