Shugaba Tinubu Ya Karawa Ma’aikata Alawus a Yunkurin Hana ‘Yan Kwadago Yajin Aiki

Shugaba Tinubu Ya Karawa Ma’aikata Alawus a Yunkurin Hana ‘Yan Kwadago Yajin Aiki

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin kudi a kan alawus da za a rika biyan ma’aikatan gwamnati
  • A maimakon N25, 000, gwamnatin tarayya ta amince a rika biyan N35, 000 na tsawon watanni shida
  • Kudin da za a bada zai shafi rukunin duka ma’aikata, akasin abin da shugaban kasa ya fara sanarwa

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bakin kokarinsa na ganin an daina maganar shiga yajin-aikin da sai baba-ta-gani a kasar nan.

Sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasar cewa an amince ayi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya karin N10, 000 kan alawus din da za a raba.

Da farko an ji labari N25, 000 da shugaba Bola Tinubu ya yi magana a kai za ta shafi duk wani ma’aikaci, akasin jawabin ranar bikin 'yancin kai.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima Hoto:@NTANewsNow
Asali: Twitter

Ma'aikata sun yarda da karin?

A yammacin Litinin kuma sai aka sake fitar da sanarwar kara adadin alawus din daga N25, 000 zuwa N35, 000 da za a biya na watanni shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta ce da alama kungiyoyin kwadago ba su yi na’am da tayin nan da aka zo da shi ba.

Wata majiya ta shaida cewa ma’aikatan kasar nan a karkashin NLC da TUC sun fadawa wakilan gwamnatin tarayya duk abin da su ke bukata.

Za a komawa wajen Bola Tinubu

Bangaren gwamnati zai gabatar da bukatun ‘yan kwadagon ga shugaba Bola Tinubu wanda yake da wuka da namar da za ta hana yin yajin-aiki.

Gwamnatin tarayya ta ce tayi karin ne duba da tattaunawar da ake yi da ma’aikata a dalilin tashin farashin man fetur a sakamakon cire tallafi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Sanar Da Karin Albashi Ga Dukkan Ma’aikata Bayan Ganawar FG Da Kungiyar Kwadago

Jagororin ‘yan kwadago a zaman da aka yi na awanni hudu su ne; Joe Ajaero, Dr Tommy Etim Okon, Emma Ugboaja, uhu Toro da sauransu.

Za a kafa wani karamin kwamiti da zai duba kokarin da gwamnati ta ke yi domin rage radadin da cire tallafin man fetur ya kawowa ma’aikata.

Legit.ng Hausa ta fahimci ma’aikata su na bukatar a kara albashi zuwa N200, 000 a Najeriya.

Yadda taron NLC, TUC da FG ya gudana

Femi Gbajabiamila ya jagoranci bangaren gwamnatin Bola Tinubu tare da gwamnoni irinsu Abdulrazak Abdulrahman da Dapo Abiodun.

Ministoci kamar Simon Lalong, Nkeiruka Onyejeocha, Atiku Bagudu, Betta Edu da Doris Uzoka-Anite su na wajen taron da aka yi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel