Dalibai 14 Cikin 24 da Aka Sace a Jami’ar Kogi Sun Kubuta, ’Yan Sanda Sun Yi Bayani

Dalibai 14 Cikin 24 da Aka Sace a Jami’ar Kogi Sun Kubuta, ’Yan Sanda Sun Yi Bayani

  • Kwanaki akalla hudu kenan da yin garkuwa da daliban jami'ar kimiyya da fasaha ta Confluence (CUSTECH) da ke Osara a jihar Kogi
  • Rundunar 'yan sandan jihar Kogi, ta ce jami'an tsaro, ciki har da mafarauta, sun yi nasarar kubutar da dalibai 14 cikin 24 da aka sace
  • A yayin da rundunar ta sha alwashin kubutar da sauran daliban, gwamnatin jihar ta kuma shaida ce wani mutane biyu sun samu rauni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kogi - An kubutar da dalibai 14 na jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence (CUSTECH) da ke Osara a jihar Kogi, wadanda ‘yan bindiga suka sace a daren ranar Alhamis.

Bethrand Onuoha, kwamishinan ‘yan sandan jihar da ke Arewa ta tsakiya ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Lokoja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 4 da jami’an FRSC a wani kazamin hari a Enugu

An kubutar da dalibai 14 da aka yi garkuwa da su a jami'ar Kogi
Jami'an tsaro sun ceto dalibai 14 daga cikin 24 da aka sace a jami'ar jihar Kogi. Hoto: Custechng
Asali: Facebook

Mun ruwaito maku cewa ‘yan bindigan sun sace daliban CUSTECH ne a lokacin da suke karatun fara jarabawar zangon farko na wannan shekarar, rahoton jaridar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalibai 24 ne aka yi garkuwa da su

Bethrand Onuoha ya ce:

“Tawagar jami’an tsaro da suka hada da mafarauta da suka bi bayan ‘yan bindigar sun yi nasarar ceto 14 daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su.
“Daya daga cikin daliban da aka ceto ya shaida mana cewa dalibai 24 ne aka yi garkuwa da su.
“Jami’an tsaro ba za su huta a kan wannan lamari ba. Za mu tabbata an kubutar da sauran daliban da ransu."

Mafarauci da jami'in tsaro sun raunata

Jaridar Leadership ta ruwaito kwamishinan yada labarai, Kingsley Fanwo, wanda shi ma ya tabbatar da ceto daliban, ya ce a halin yanzu daliban 14 na samun kulawar da ya kamata.

Kara karanta wannan

Mazauna Port Harcourt sun damu da rikicin Wike da Fubara, sun mika bukata ga alkalai

Ya bayyana farin cikinsa da cewa an fara ceto daliban ne sa’o’i bayan da Gwamna Usman Ododo ya ziyarci jami'ar tare da ba iyaye tabbacin cewa za a kubutar da daliban da aka sace.

“Sai dai akwai wani mafarauci da kuma wani jami’in tsaro da suka samu raunuka a yayin fafatawa da 'yan bindigar lokacin da aka je ceto daliban. Yanzu haka suna asibiti."

- A cewar Fanwo.

Dan ta'addan Boko Haram ya mika wuya

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa, wani dan ta'addan Boko Haram mai suna Alhaji Wosai ya mika wuya ga sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai a jihar Borno.

Alhaji Wosai wanda ya tsere daga maboyar ‘yan ta’addan a kauyen Garno da ke jihar ya kuma mika bindigarsa kirar AK47 guda 1 da tarin alburusai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel