Yadda Dakarun Sojoji Suka Dakile Harin da Yan Ta'adda Suka Kaiwa Ayarin Gwamnan APC a Arewa

Yadda Dakarun Sojoji Suka Dakile Harin da Yan Ta'adda Suka Kaiwa Ayarin Gwamnan APC a Arewa

  • Hedikwatar tsaron ƙasa ta bayyana yadda sojoji suka daƙile harin da yan ta'adda suka kaiwa ayarin Gwamna Buni na jihar Yobe
  • A ranar Asabar da ta gabata ne yan ta'adda suka farmaki ayarin motocin gwamnan na APC a hanyar zuwa Damaturu
  • Manjo Janar Buba ya ce ɗan sanda ɗaya daga cikin waɗanda suka ji raunuka ya rasu bayan kwantar da shi a Asibiti

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojin rundunar 29 Task Force Brigade sun samu nasarar daƙile harin da ƴan ta'adda suka kaiwa ayarin gwamnan jihar Yobe.

Sojoji sun dakile harin yan ta'adda kan ayarin Gwamna Buni.
Yadda Sojoji Suka Dakile Harin da Yan Ta'adda Suka Kaiwa Ayarin Gwamnan Yobe Hoto: DHQ, Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Hedkwatar tsaron ƙasa ta ce gwarazan dakarun sojin sun dakile harin da ƴan ta'addan suka kaiwa ayarin Gwamna Mala Buni a titin Maiduguri zuwa Damaturu ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Mataimakin Shugaban APC ya faɗi kujerar gwamnan da zasu ƙwace a arewa

Mai magana da yawun DHQ na ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yi bayanin cewa dakarun sojojin sun ɗauko motoci biyu da harin ƴan ta'addan ya shafa.

Ya ce direban babbar motar soji guda daya, ‘yan sanda hudu masu rakiya da jami’in hukumar tsaron farin kaya (DSS) daya da suka samu raunuka a harin na cikin koshin lafiya.

Shin an samu asarar rayuka a harin?

A cewarsa, ɗaya daga cikin ƴan sandan da suka samu rauni a harin ya mutu jim kaɗan bayan an kai shi asibitin ƙwararru da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Buba ya ce:

"Yanzu haka ƙarin dakarun sojin rundunar Birged ta 29 karkashin jagorancin kwamadan rundunar sun ƙara matsa kaimi domin zaƙulo maharan da suka aikata wannan ɗanyen aiki."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya roƙi 'yan Najeriya muhimmin abu 1 da zai taimaka wajen yaƙar ta'addanci a arewa

"Motocin da harin ya shafa waɗanda suka kunshi motar sojoji ɗaya da ta fararen hula da aka harbi tayoyinta a harin, yanzu an ɗauko su zuwa sansanin sojojin Benisheikh."

Idan baku manta ba ƴan ta'adda sun kai harin kwantan ɓauna kan ayarin Gwamna Buni ranar Asabar yayin da yake hanyar komawa Damaturu daga Maiduguri.

The Cable ta tattaro cewa gwamnan ba ya cikin ayarin a lokacin harin, amma sakataren gwamnatin Yobe da saura kusoshin gwamnati da lamarin ya rutsa da su sun tsira.

Gwamnan PDP ya yi amai ya lashe kan tsige CJ

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Osun ya canza shawara kan tsige shugaban alkalan jihar da kuma naɗa wanda zai maye gurbinsa.

Adeleke ya rubuta wasika ya aike wa Alkalin alkalan Najeriya (CJN) kan matsayar majalisar dokokin jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel