Hatsabiban Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin da Suka Kai Hari a Jihar Arewa
- Yan bindiga huɗu sun bakunci lahira yayin da suka kai farmaki kauyen Ɗan Umaru a jihar Kebbi ranar Litini
- Jami'an rundunar ƴan banga ne suka yi nasarar halaka ƴan bindiga bayan sun musu kwantan ɓauna
- Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Jami'an tsaro ƴan sa'kai waɗanda aka fu sani da 'yan banga ko 'yan bijilanti sun samu nasarar halaka yan bindiga huɗu a jihar Kebbi, Arewa maso Yamma.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ƴan bangan sun murƙushe yan bindigan ne yayin da suka farmaki wani mutumi a ƙauyen Ɗan-Umaru, yankin Bena a jihar Kebbi ranar Litinin.
Sakataren watsa labaran gwamnan jihar, Ahmed Idris ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Litinin a Birnin Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idris ya ce wannan nasara da aka samu ta fito ne daga bakin babban daraktan tsaro na majalisar zartarwa ta jihar Kebbi, AbdulRahman Usman.
Yadda aka kashe maharan gaba ɗayansu
Ya ce ‘yan banga sun dauki matsayi tare da kashe ‘yan bindigar a lokacin da suka kai farmaki wani kauye da ke kusa da Dan-Umaru mai iyaka da ƙauyen Dadin Duniya a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Ya kara da bayanin cewa a halin yanzu mutumin da harin ya shafa na kwance ana duba lafiyarsa a wani asibiti da ba a bayyana ba.
A kalamansa ya ce:
"Lokacin da 'yan bindigan suka kaddamar da hari a ƙauyen, cikin hanzari 'yan bangan suka ɗauki matsaya, kana suka ɗana wa maharan tarko suka sheƙe su dukka huɗun."
"Gawarwakin yan bindigan na can a ƙauyen Ɗan Umaru amma lamarin ya faru ne a kusa da ƙauyen wanda ke iyaka da ƙauyen Dadin Duniya na ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara."
An sace fasinjojin motar Gwamnatin Benue
A wani rahoton na daban kuma Miyagun ƴan bindiga sun sace mutane 13 daga motar kamfanin sufuri ta Gwamnatin jihar Benuwai.
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun tare motar Bas ɗin a titin Naka zuwa Makurdi ɗauke da fasinjoji 16, uku suka tsira.
Asali: Legit.ng