Dakarun Sojin Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 100, Sun Samu Nasarori Masu Yawa

Dakarun Sojin Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 100, Sun Samu Nasarori Masu Yawa

  • Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda 113, kuma sun kamo wasu 300 a makon da ya gabata a faɗin kasar nan
  • Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce bayan haka sojojin sun kwato mutane 91 da aka yi garkuwa da su
  • A cewarsa, wannan karon an samu haɗin kai tsakanin sojojin sama da na ƙasa irin wanda ba a taɓa samunsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta samu nasarar murƙushe ƴan ta'adda 113 tare da kamo wasu 300 a cikin mako ɗaya a sassan ƙasar nan.

Sojojin Najeriya.
Dakarun Soji Sun Halaka Yan Ta'adda 113, Sun Damke Wasu 300 Cikin Mako Ɗaya Hoto: NigerianArmy
Asali: Facebook

Bayan haka, Dakarun sojin sun kuma ƙwato mutane 91 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a wannan lokaci, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙara kai hari kan ɗaliban jami'ar Tarayya, sun tafka ɓarna yayin da suka buɗe wuta

Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana waɗannan nasarori a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba ya kuma bayyana cewa sojoji sun kama mutane 25 da ake zargin ɓarayin ɗanyen man fetur ne, tare da lalala haramtattun matatun mai 49 a makon jiya.

Kakakin sojin ya yi bayanin cewa bayan haka sun kuma yi nasarar ƙwato man da ɓarayin suka sace wanda ya kai kimanin N571,793,350.00.

Ya ce sojojin sun ƙara da kwato makamai iri-iri guda 129 da alburusai kala daban-daban guda 717 daga hannun ƴan tada ƙayar baya, rahoton PM News ya tattaro.

Zamu kawo karshen ta'addanci - Sojoji

Janar Buba ya ce dakarun sojin kasar za su ci gaba da matsa wa kungiyoyin tada ƙayar baya lamba da nufin samar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke ƴan ta'adda 10 a Kaduna, sun kwato makamai masu yawa

Kakakin sojin ya ce:

"Ko shakka babu dole ne a ci galaba a kan wadannan kungiyoyi, kuma lalle ana cin nasara a kan su."
"Saboda wadannan dalilai ne muke yiwa ‘yan ta’adda, ‘yan tada kayar baya da masu tsattsauran ra’ayi mummunar barna ta hanyar samamen da muke kai musu a fadin kasar nan."
"An samu haɗin kai tsakanin sojojin sama da na ƙasa kamar wanda ba a taɓa gani ba kuma yana haifar da sakamako da nasarori masu ban mamaki."

Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Motar Ɗalibai Wuta

A wani labarin kuma Wasu mutane ɗauke da bindigu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan motar ɗaliban makaranta a jihar Enugu.

An tattaro cewa maharan sun kashe ɗaliba mace ɗaya yayin da wasu da dama su ke kwance rai hannun Allah a Asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262