Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugabar Karamar Hukuma a Jihar Benue

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugabar Karamar Hukuma a Jihar Benue

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da shugabar ƙaramar hukumar Okpokwu da aka dakatar a jihar Benuwai, Amina Audu
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace matar ne yayin da take hanyar Naka zuwa Makurdi da safiyar ranar Litinin
  • A cewar dakataccen shugabana ƙaramar hukumar Ado, har yanzu ƴan bindigan ba su kira kowa kan lamarin ba

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Miyagun ƴan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun sun yi garkuwa da dakatacciyar shugabar ƙaramar hukumar Okpokwu a jihar Benuwai, Amina Audu.

Yan bindiga sun sace shugabar karamar hukuma a Benue.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugabar Karamar Hukuma a Jihar Benue Hoto: dailypost
Asali: UGC

Jaridar Punch ta tattaro cewa maharan sun yi awon gaba da tsohuwar Ciyaman ɗin tare da direbanta da safiyar ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan bindiga sun mutu yayin da dakarun sojoji suka buɗe musu wuta a jihar Arewa

Ganau ya bayyana cewa Amina na cikin tafiya a titin Naka zuwa Makurɗi, kwatsam ƴan bindigan suka yi kwantan ɓauna a dai-dai Tyolaha Ahume, suka tafi da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ƴan bindigan sun buɗe wa motar da matar ke ciki wuta, wanda ya tilasta musu tsayawa.

"Nan take ƴan bindigan suka fito da matar da kuma mai tuƙa motar, sannan suka tasa su zuwa cikin daji," in ji mutumin.

Shin maharan sun tuntuɓi dangi?

Haka nan kuma yayin da aka tuntuɓi abokin aikinta, dakataccen shugaban ƙaramar hukumar Ado, James Oche, ya tabbatar da sace Amina Audu, ga yan jarida.

Jaridar Daily Post ta rahoto shi yana cewa:

"Eh da gaske ne, na fahimci cewa an yi garkuwa da ita tare da direbanta, kuma har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntuɓi kowa ba."

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum 2 tare da sace babban malamin addini a jihar Kwara

Duk wani yunƙuri na jin ta bakin jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, bai kai ga nasara ba domin ta ƙi ɗaga kiran wayar tarho.

Da aka tuntubi mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Mista Joseph Har, ya ce “bani da cikakken bayani, zaku iya kiran PPRO."

Dakarun Sojin Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Uku a Jihar Kaduna

A wani rahoton na daban Sojojin Najeriya sun ragargaji ƴan bindiga a garuruwa da dama a jihar Kaduna, sun yi nasarar kashe wasu, sun kwato makamai.

Mataimakin daraktan yaɗa labarai, Musa Yahaya, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne yayin da suka fita aikin shara ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel